Dalilin da yasa Shugaba Buhari zai amince da sauya Kundin Tsari - Dogara, Saraki

Dalilin da yasa Shugaba Buhari zai amince da sauya Kundin Tsari - Dogara, Saraki

A ranar Alhamis din da ta gabata ne, shugabanni biyu na majalisar dokoki ta tarayya, Bukola Saraki da Yakubu Dogara, sun bayyana cewa tuntube-tuntube da shawarwarin 'yan Najeriya zasu tilasta shugaba Buhari amincewa da sauya Kundin Tsari.

Shugabannin biyun sun bayyana cewa, shawarwarin 'yan Najeriya na sauya wasu sassa cikin Kundin Tsarin mulkin kasa na shekarar 1999 zasu wajabtawa shugaba Buhari amincewa da yin gyara da kuma kyautata shi domin ciyar da kasar nan gaba.

Saraki tare da Shugaba Buhari

Saraki tare da Shugaba Buhari

Saraki da Dogara sun bayyana hakan ne a yayin karbar sakamakon ra'ayoyin majalisun dokoki na jihohin kasar nan dangane da sauya Kundin Tsarin mulki.

KARANTA KUMA: Ba bu laifin da Magu yayi kuma yana nan daram - Osinbajo

Dogara ya kara da cewa, a halin yanzu shugaba Buhari ba ya da wani zabi face amincewa da sauya Kundin Tsarin domin cikar burin 'yan Najeriya.

Jaridar NAIJ.com ta kuma ruwaito cewa, wasu 'yan Najeriya sun bayyana korafe-korafen su yayin dawowar Yusuf Buhari daga jinya a asibitar wata kasar ketare da fadar shugaban kasa ba ta bayyana ta ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Jam'iyyar PDP ne neman a tsige Sanatanta da ya sauya sheka zuwa APC

Bayan ya sauya sheka zuwa APC, PDP ne neman tsige Sanata Akpabio

Bayan ya sauya sheka zuwa APC, PDP ne neman tsige Sanata Akpabio
NAIJ.com
Mailfire view pixel