Yanzu-Yanzu: An kashe wani babban kwamandan sojojin Najeriya a dajin Sambisa

Yanzu-Yanzu: An kashe wani babban kwamandan sojojin Najeriya a dajin Sambisa

Kamar dai yadda muka samu daga majiyar mu ta bayyana cewa dakarun kasar Najeriya sun yi babban rashi na daya daga cikin manyan jiga-jigan kwamnadojin ta da ke yaki da 'yan ta'addan Boko Haram da suka addabi yankin arewa mmaso gabas a dajin Sambisa mai suna Laftanal Kanal A E Mamudu.

Haka ma dai Majiyar ta mu dai har ila yau ta bankado mana cewa yau din nan ne dai babban kwamnantan ya rasu tare da wani matashin sojan ruwa yayin da suke wani sintiri a dajin na Sambisa.

Yanzu-Yanzu: An kashe wani babban kwamandan sojojin Najeriya a dajin Sambisa
Yanzu-Yanzu: An kashe wani babban kwamandan sojojin Najeriya a dajin Sambisa

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya tayi karin haske game da karin albashi

Legit.ng dai haka zalika ta samu cewa babban kwamandan wannan ne karo na biyu da aka tura shi yankin na arewa maso gabashin kasar domin yaki da 'yan ta'addan Boko Haram din.

Haka nan ma kuma an bayyana Laftanal KanaL Mamudu a matsayin wani zaki da bai da tsoro a filin daga.

A wani labarin kuma, Kungiyar nan ta addinin Islama ta Jama’atu Nasril Islam karkashin jagorancin Sarkin musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar na III a jiya Alhamis sun yi tofin Allah tsine ga gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari game da satar 'yan matan makarantar Dapchi 110.

Kungiyar dai ta bayyana cewa wannan sakacin na gwamnati abun takaici ne kuma ya kawo koma baya ga ilimin 'ya'ya mata a yankin na Arewacin Najeriya wanda kuma hakan ba karamin nakasu bane ga yankin.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel