Ba bu laifin da Magu yayi kuma yana nan daram - Osinbajo

Ba bu laifin da Magu yayi kuma yana nan daram - Osinbajo

Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa Ibrahim Magu, mukaddashin shugaban hukumar hana yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC bai aikata laifin komai ba kuma yana nan daram babu wanda zai sauke shi daga mukamin sa.

Tuni dai Majalisar Dattawa da bukaci a sauya kujerar Magu da wani shugaban, sakamakon rashin samun nasarar tantancewa da ta yi masa har karo biyu a baya, sai dai duk da hakan fadar shugaban kasa ta ci gaba da rikon sa a matsayin shugaban hukumar.

Domin nuna rashin amincewar wannan matsaya ta fadar shugaban kasa akan shugaban hukumar na EFCC, majalisar dattawan ta dakatar da tantance zababbun shugabannin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada, wanda wannan lamari ya kawo tsaiko cikin gudanar da wasu al'amurra da shawarwari na gwamnati.

Farfesa Yemi Osinbajo

Farfesa Yemi Osinbajo

A yayin ganawar ranar Alhamis da manema labarai a fadar shugaban kasa ta Villa, Mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya bayyana cewa, babu wani laifi da Magu ya aikata hakazalika yana daram a kujerar sa ba tare da amincewar Majalisar ta Dattawa ba.

KARANTA KUMA: Majalisar wakilai ta juya baya ga Kayode Fayemi da mataimakin sa

Jaridar The Cable ta kuma ruwaito cewa, wannan ba shine karo na farko da mataimakin shugaban kasar ya saba kare Magu a bainar jama'a ba, sakamakon sanayya tare da amincin dake tsakanin su.

Jaridar NAIJ.com ta kuma ruwaito cewa, wasu 'yan Najeriya sun bayyana korafe-korafen su a fili yayin dawowar Yusuf Buhari daga jinya a wata kasar waje da fadar shugaban kasa ba ta bayyana ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hari la yau: ‘Yan bindiga a Kaduna sun sace matar malamin addini bayan sun kashe shi

Masu garkuwa sun sace matar wani malamin addini a Kaduna bayan sun kashe shi

Hari la yau: ‘Yan bindiga a Kaduna sun sace matar malamin addini bayan sun kashe shi
NAIJ.com
Mailfire view pixel