Da dumin sa: An gano gidajen alfarma 2 na Sanata Ekweremadu a birnin Landan

Da dumin sa: An gano gidajen alfarma 2 na Sanata Ekweremadu a birnin Landan

Wasu bayanan sirri da muka samu daga majiyar mu ta Sahara Reporters ta tabbatar da cewa an gano wasu gidajen alfarma masu tsadar gaske har guda biyu a birnin Landan na kasar Ingila mallakar mataimakin shugaban majalisar dattijan Najeriya, Ike Ekweremadu.

Gidajen dai kamar yadda muka samu daga ma'aikatar da ke kula da filaye ta kasar Ingila din dai gidajen na da adreshi ne karmar haka: "52 Aylestone Avenue, London, NW6 7AB da kuma Flat 4, Varsity Court, 44, Homer Street, London, W1H 4NW.

Da dumin sa: An gano gidajen alfarma 2 na Sanata Ekweremadu a birnin Landan
Da dumin sa: An gano gidajen alfarma 2 na Sanata Ekweremadu a birnin Landan

KU KARANTA: Mutum dubu 10 sun koma APC a jihar Edo

Legit.ng dai ta samu cewa wannan ba shine karo na farko da ake gano manyan gidajen alfarma ba mallakin 'yan Najeriya a kashen waje ba wanda hakan na nuni ne da irin tsabar cin hanci dake gudana a kasar.

A wani labarin kuma, Majalisar wakilan Najeriya a yau sun yi tofin Allah-tsine tare da nuna rashin gamsuwa da salon mulki na ministocin gwamnatin shugaba Buhari dake da alhakin kula da ma'adinai da karafa watau Mista Kayode Fayemi da kuma mataimakin sa Abubakar Bwari.

'Yan majalisun dai a yayin zaman na su na yau sun kuma yi kakkausan furuci ga ministocin bisa ga kin mutunta kiran da suka yi masu suyi masu bayani kan yadda harkar kamfanin karafa na Ajaokuta yake.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel