Rikita-Rikita: Majalisar wakillai sun yi tofin Allah-tsine ga ministocin Buhari 2

Rikita-Rikita: Majalisar wakillai sun yi tofin Allah-tsine ga ministocin Buhari 2

Majalisar wakilan Najeriya a yau sun yi tofin Allah-tsine tare da nuna rashin gamsuwa da salon mulki na ministocin gwamnatin shugaba Buhari dake da alhakin kula da ma'adinai da karafa watau Mista Kayode Fayemi da kuma mataimakin sa Abubakar Bwari.

'Yan majalisun dai a yayin zaman na su na yau sun kuma yi kakkausan furuci ga ministocin bisa ga kin mutunta kiran da suka yi masu suyi masu bayani kan yadda harkar kamfanin karafa na Ajaokuta yake.

Rikita-Rikita: Majalisar wakillai sun yi tofin Allah-tsine ga ministocin Buhari 2

Rikita-Rikita: Majalisar wakillai sun yi tofin Allah-tsine ga ministocin Buhari 2

KU KARANTA: Najeriya ta kai jami'ar Amurka kara kotu

NAIJ.com ta samu cewa 'yan majalisar sun bayyana kin zuwan na su a matsayin wani rainin hankali tare kuma da sakaci da aikin su musamman ma ganin yadda kamfanin yake da alaka sosai da cigaban habakar tattalin arzikin kasa.

A wani labarin kuma, Wata kotun tarayyar dake zaman ta a unguwar Maitama, garin Abuja, babban birnin tarayya ta baiwa Sanata Dino Melaye dake zaman dan majalisar dattijai dake wakiltar jihar Kogi da aka gurfanar a gaban ta bisa laifin sharara karya ga hukuma belin Naira dubu 100.

Tun farko dai an gurfanar da dan majalisar ne bisa laifuka biyu da suka hada da shararwa gwamnati karya wajen bayar da bayanai na cewar an kai masa hari a shekarar bara, zargin da Sanatan kuma ya karyata.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain NAIJ.com HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Jam'iyyar PDP ne neman a tsige Sanatanta da ya sauya sheka zuwa APC

Bayan ya sauya sheka zuwa APC, PDP ne neman tsige Sanata Akpabio

Bayan ya sauya sheka zuwa APC, PDP ne neman tsige Sanata Akpabio
NAIJ.com
Mailfire view pixel