Badakalar dala miiyan 44: Magu zai sha tambayoyi a majalisar wakilai na tsawon awanni 2

Badakalar dala miiyan 44: Magu zai sha tambayoyi a majalisar wakilai na tsawon awanni 2

A ranar Laraba 14 ga watan Maris ne majalisar wakilai za ta gudanar da wani zaman bincike game da kudi dala miliyan 44 da ake zargin sun yi batan dabo a hukumar leken asir, NIA, inji rahoton Daily Trust.

KU KARANTA: Ta leƙo ta koma: Amarya ta fasa auren Angonta bayan ta gane yana da sanƙo kwana ɗaya kafin ayi biki

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito yan majalisar zasu tattauna ne da shugaban hukumar yaki da rashawa da yai ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, inda suka ce ya zama wajibi Ibrahim Magu ya amsa tambaya tunda hukumar ce ta fara gano sauran kudin, dala miliyan 43 a wani gida a jihar Legas.

Badakalar dala miiyan 44: Magu zai sha tambayoyi a majalisar wakilai na tsawon awanni 2

Majalisa

Majalisar ta hannun kwamitin kula da hukumomin tsaro na sirri na binciken musabbabin bacewar wadannan kudade ne daga hukumar ta NIA, tare da yadda aka yi shugaban hukumar na yanzu, Ahed Rufai ya dare mukamin.

Shugaban kwamitin, Aminu Sanin Jaji, dan majalisa daga jihar Zamfara ne ya bayyana haka ga manema labaru a babban birnin tarayya, inda yace zasu nemi karin haske daga haske daga sauran hukumomin da abin ya shafa don gano bakin zaren.

Tun bayan rantsar da sabon shugaban hukumar NIA, Ahmed Rufai ne aka fara samun korafe korafe daga ciki da wajen hukumar kan rashin dacewarsa da mukamin, haka zalika ana zarginsa da hada kai da wasu shafaffu da mai dake fadar shugaban kasa wajen yin sanadin bacewar dala miliyan 44.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hari la yau: ‘Yan bindiga a Kaduna sun sace matar malamin addini bayan sun kashe shi

Masu garkuwa sun sace matar wani malamin addini a Kaduna bayan sun kashe shi

Hari la yau: ‘Yan bindiga a Kaduna sun sace matar malamin addini bayan sun kashe shi
NAIJ.com
Mailfire view pixel