Jerin sababbin fim din Hausa a 2017-2018

Jerin sababbin fim din Hausa a 2017-2018

Sababbin wasannin Hausa na ci gaba da samun krbuwa. Wannan ya sa kamfanin shirya fina-finan Hausa kara samun kudi da suke shirya wasanni masu inganci sosai. Masana’antar na da masoya da dama, jarumai da kuma daraktoci masu fasaha.

Jerin sababbin fim din Hausa a 2017-2018

Sababbin fim a 2017

1. Kanwar Dubarudu

A cikin wannan fim akwai manyan jarumai kamar Rahama Sadau da Ali Nuhu. Rahama da Ali Nhu sun hau matakin yaya da kanwa wanda zasu iya sadaukar da komai ga junansu.

2. Auren Manga

Wannan wasa ne da ba’a gajiya da kallo. Wani jarumi Suleiman Yahaya Bosho ya kasance tauraron wannan fim inda ya hau matakin jami’in dan sanda. Falalu Dorayi ne ya yi daraktaan wannan fim mai tarin barkwanci.

3. Mansoor

Umar Shareef ne ya zamo tauraron wanan fim. Ya fada tarkon soyayya, amma abubuwaa da dama sun faru da wannan labara na soyayya. Ali Nuhu, Garzali Miko, Baballe Hayatu sun kasance a fim din.

4. Rariya

Rahama Sadau ta shirya wannan fim mai tarin takwa, ado da kuma rawa na zamani.

5. Mijin Yarinya

Tauraron wannan wasa ya kasance wani tsoho da yake shawarar auran yarinya karama.

KU KARANTA KUMA: Operation Cat Race: Sojoji sun gargadi jama’a

Sababbin fim a 2018

1. Aljannar Duniya

Ya hada jarumai irin su Fati K.K Usman, Yakubu Muhammad. Labarin wani mutumi ne da yayi kokarin taimako, amma sai abun ya juye a kanshi.

2. Dare Daya

Akwai jarumai kamar su Sha'Aibu Lawan, Rabiu Rikadawa a ciki. Labarin wasu ma’aurata ne da suka fuskanci kalubale da iyalansu amma sun shawo kan komai.

3. Kalamu Wahid

Akwai jarumai irin su, Sadiq Ahmad, Ali Nuhu, Lawan Ahmad, Samira Abubakar. Labarin wani mutumi ne day a ziyarci abokinsa daga nan sai labara ya sha bambam.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel