Rikicin jihar Kaduna: An banka ma gidajen wani kauye wuta

Rikicin jihar Kaduna: An banka ma gidajen wani kauye wuta

Rikicin jihar Kaduna ya cigaba da ruruwa a yankunan makwabtan kasuwar magani, asalin inda rikicin ya faro kenan, a cikin karamar hukumar Kajuru na jihar, inji rahoton jaridar Premium Times.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito an samu kataniya a kauyen Kalla duk a cikin karamar hukumar Kajuru, inda aka kona gidake sama da 300, inda a yanzu haka jama’a da daman a gudun hijira a wajen yan uwa da abokan arziki.

KU KARANTA: Sanata Abdullahi Adamu ya bukaci masu yiwa gwamnatin Shugaba Buhari zagon kasa dasu fice daga jam'iyyar APC

Mazauna garin sun bayyana cewar da misalin karfe 5 na yammacin ranar Talata 27 ga watan Feburairu ne matasa suka dinga bi suna banka ma gidajen wuta. Haka zalika wani mazaunin garin mai suna Akilu da ya zanta da majiyarmu yace a ofishin Yansanda shi da iyalansa suka nemi mafaka.

Rikicin jihar Kaduna: An banka ma gidajen wani kauye wuta
Rikicin jihar Kaduna

“A ranar Talata da aka yi rikicin a kasuwar magani, babu abinda ya faru a garinmu, daga bisani kuma matasa suna banka bin gida gida suna banka musu wuta, da kyar muka ci sa’a Yansanda suka kawo mana dauki.” Inji shi.

Sai dai Akilu yace babu wanda aka kashe a rikicin, sai dai wani dattijo da aka raunata; “Muna zaman lafiya da kabilun yankin mu, amma bana ganin zan kara komawa kauyen.” Haka zalika an dakatar da masu ababen hawa dake bin hanyar Kaduna-Kachia-Kajuru don gudun fadawa cikin rikicin.

Rikicin jihar Kaduna: An banka ma gidajen wani kauye wuta
Rikicin jihar Kaduna

A kokarinsu na wayar da kan jama’a akan illar fadace fadace, shugaban gidauniyar dawo da zaman lafiya na Najeriya, Fasto Yohanna Buru ya gana da shuwagabannin Musulmai da Kirista, inda suka bayyana ma jam’a cewa zaman lafiya ne maganin duk wasu matsalolin Najeriya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel