An damke wani David Paul, mai hada bindigogi a kudancin jihar Kaduna

An damke wani David Paul, mai hada bindigogi a kudancin jihar Kaduna

Jam’ian atasa’in Operation Safe Haven a jihar Falto sun damke wani manomi wanda ya kware wajen hada bindigogi a jihar Kaduna.

Kakakin rundunar, Major Adam, ya bayyana cewa manomin mai suna David Paul ya shiga hannu ne a kauyen Kabu, karamar hukumar Jema’a a kudancin jihar Kaduna.

Ya bayyana cewa sun damkeshi ne da bindigogi 50 wanda ya kunshi manya da kanana sakamakon wani cinne daga cikin jama’a.

“Bincike na kai yanzu domin kama abokan aikinsa da kuma masu sayan makamansa. Za’a mikashi ga hukumar yan sanda a Kaduna domin cikakken bincike.” Ya ce.

An damke wani David Paul, mai hada bindigogi a kudancin jihar Kaduna

An damke wani David Paul, mai hada bindigogi a kudancin jihar Kaduna

David Paul ya bayyana cewa ya kasance cikin wannan sana’a shekaru 15 kenan. Ya kara da cewa hukuma bata taba kamashi ba duk da cewa yana sayar da makamansa a kasuwa.

KU KARANTA: Kun kunyata yan Najeriya, Dino Melaye ya caccaki APC

“Na kan ga yan sanda suna wucewa kuma suna gani na. Sai suce ‘kalli mutumin nan mai hada makamai,’ basu taba ce min ya saba doka ba. Yawancin makaman an kawo gyara ne amma na kan hadawa mafarauta.”

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a: https://facebook.com/naijcomhausa https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
2019: Atiku ya yi alfahari da kwarewar sa a warware wata matasalar da ya ce tafi damun Najeriya

2019: Atiku ya yi alfahari da kwarewar sa a warware wata matasalar da ya ce tafi damun Najeriya

2019: Atiku ya yi alfahari da kwarewar sa a warware wata matasalar da ya ce tafi damun Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel