Kun kunyata yan Najeriya, Dino Melaye ya caccaki APC

Kun kunyata yan Najeriya, Dino Melaye ya caccaki APC

Sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta yamma a majalisar dattawan Najeriya, Dino Melaye, ya caccaki jami’yyarsa na APC da rashin cika alkawuran da akayiwa yan Najeriya.

Sanata Dino Melaye ya fito karara ya soki jam'iyyarsa na APC kan mawuyacin halin da yan Najeriya ke ciki.

“Gwamnatin APC ta zama hukumar koke-koke. Ina fadan wannan ba tare da tsoro ba. Koke-koke sun fi yawa a APC da fadar shugaban kasa fiye da ayyukan da akayi. Ba zai yiwu mu cigaba da haka ba. Shugaban kasa ya fadi kwanaki biyu da suka gabata ya ce mu zanna lafiya amma ina mai cewa, ba zai yiwu a zauna lafiya ba cikin zalunci.

Al’umma na cikin yunwa, akwai talauci ko ina, kuma ga rashin aikin yi da yayi yawa. Ba’a yanke shawari ba, kuma ana saon zaman lafiya. Babban hakkin gwamnati shine tsaron jama’a da jin dadinsu. Babu tsaro kuma babu jin dadi,”. Yace

Kun kunyata yan Najeriya, Dino Melaye ya caccaki APC

Kun kunyata yan Najeriya, Dino Melaye ya caccaki APC

Ya kara da cewa Najeriya na cikin mawuyacin halin rashin lafiya. Wajibi ne a kawo gyara. Yin shiru zalunci ne idan abubuwan da bai dace ba na faruwa.

KU KARANTA: Mashawartan shugaba Buhari na kawo koma baya a Najeriya

Zaku tuna cewa mutane sun caccaki sanata Dino Melaye akan yin alfaharin ginawa al’ummarsa wani kwalbati da sunan gada. Jama’an sun ce yan siyasanmu sun rainawa jama’ansu hankali idan har ana alfahari da abubuwa irin wannan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a: https://facebook.com/naijcomhausa https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Rikicin wani Gwamnan APC da Mataimakin sa ya kai makura

Rikicin wani Gwamnan APC da Mataimakin sa ya kai makura

Rikicin wani Gwamnan APC da Mataimakin sa ya kai makura
NAIJ.com
Mailfire view pixel