Zamu cika kasuwa da kananan kudi na naira – Inji CBN

Zamu cika kasuwa da kananan kudi na naira – Inji CBN

A kokarin ganin an magance karancin kananan kudade a ranar Talata, 27 ga watan Fabrairu, babban bankin Najeriya ya fara wani shiri bisa kudirin ganin an cika kasuwanni da kananan kudade kamar su N100, N50, N20, N10 da kuma N5.

Babban bankin ya kuma yi gargadi kan boye kananan kudade, inda ya bayyana cewa duk wanda aka kama zai fuskanci hukunci mai tsanani.

Da yake Magana a wajen wani taron wayar da kai da akayi a kasuwar Wuse a Abuja, daraktan kudi na CBN, Misis Priscilla Eleja, tace babban banki bai ji dadin yadda kananan kudade sukayi karanci ba.

Zamu cika kasuwa da kananan kudi na naira – Inji CBN
Zamu cika kasuwa da kananan kudi na naira – Inji CBN

Ta bayyana cewa bankin ya damu da al’amarin sannan kuma ya yanke shawarar magance kalubalen, inda zai fara daga kan yan kasuwa.

KU KARANTA KUMA: Kasar Amurka na neman Shugaban Boko Haram Abu Musab Al-Barnawi

Ta kuma gargadi masu boye kananan kudade da kudirin samun riba wajen sake sayar dasu da su daina domin zasu fuskanci hukunci idan aka kama su.

A halin da ake ciki bankuna da dama na kasar nan za su gamu da babban cikas bayan da su ka gaza cika wani sabon sharadi da babban bankin kasar na CBN ya sa kwanan nan kamar yadda mu ka samu labari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel