Dalilan da ya sa Buhari ya ki rattaba hannu kan kudirin kafa 'Peace Corps'

Dalilan da ya sa Buhari ya ki rattaba hannu kan kudirin kafa 'Peace Corps'

- Shugaba Muhammadu Buhari ya yi watsi da kudirin kafa Hukumar Zaman Lafiya na 'Peace Corps'

- Buhari ya ce gwamnatin tarayya na fama kallubalen tsaro kana kasar ba ta da isasun kudin da za ta ware don kafa hukumar

- Buhari ya kara da cewa sauran hukumomin tsaro na Najeriya na gudanar da duk ayyukan da aka zayyana cewa sabuwar hukumar za ta yi, saboda haka maimaici ne kawai

Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da yan majalisar kasa matsayar sa kan kudirin kafa Hukumar Zaman Lafiya na Peace Corp a cikin wata wasika da ya aike kuma Kakakin Majallisar na Wakilai Dogara Yakubu ya karanta a gabar majalisar ranar Talata.

Dalilan da ya sa Buhari ya ki rattaba hannu kan kudirin kafa 'Peace Corps'
Dalilan da ya sa Buhari ya ki rattaba hannu kan kudirin kafa 'Peace Corps'

Shugaba Buhari ya bayyana matsalolin rashin tsaro da rashin isashen kudi da gwamnatin tarayya ke fama da su a halin yanzu a matsayin dalilan da ya sa ba zai iya amince wa da kudirin na kafa Hukumar Zaman Lafiyar ba.

DUBA WANNAN: Mutane 4 sun jikkata yayin da aka gabza fada tsakanin makiyaya da manoma jihar Ebonyi

Buhari ya kuma kara da cewa duk ayyukan da hukumar za tayi akwai hukumomin tsaro da ke gudanar da su a yanzu saboda hakan ya ce maimaici ne kawai.

Majalisar Tarayyah ta karanto kudirin kafa dokar ta Peace Corps ne tun a shekarar 2017 bayan an dauki lokaci mai tsawo ana dauki ba dadi tsakanin Jami'an Hukumar da sauran hukumomin tsaro na Najeriya.

Galibin yan Najeriya musamman matasa dai sun rai cewa shugaban kasan zai amince da kudirin don suna ganin kafa hukumar zai rage radadin talauci da suke fama dashi ta hanyar samar da aikin yi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel