'Yan kasuwar canji na saida Dalar Amurka a kan N362

'Yan kasuwar canji na saida Dalar Amurka a kan N362

- Dalar Amurka ba ta samu tashi sama ba a wannan makon

- Yanzu haka ana saida Dalar ne a kan N352 a kasuwar canji

- A wancan makon ma haka dai 'yan canji su ka saida Dalar

Idan mu ka koma bangaren tattalin arziki, za mu ji cewa Darajar Naira ba tayi kasa ba a wannan makon inda ake saida kowace Naira a kan Dalar Amurka a N362 kamar yadda mu ka samu labari.

Tattalin arziki: Darajar Naira ba ta kife ba a wannan makon
Dala ba ta tashi ba a wannan makon

Idan ba a manta ba a makon da ya gabata, an saida Dalar Amurka ne a kan N362. Har yanzu dai farashin bai tashi ba a kasuwar 'yan canji. Ana kuma saida EURO na Turai ne a kan N481 a hannun 'Yan canji yanzu haka a Garin Legas.

KU KARANTA: Wani ya saci kudin Gwamnati ya gina otel

Hukumar dillacin labarai na kasa watau NAN tace haka-zalika a hannun 'Yan BDC, darajar Dalar ba ta tashi ba wanan makon. Babban bankin Najeriya watau CBN na saida Dalar ne a kan N305.19 yanzu haka inji 'yan jaridar kasar.

Yanzu dai babu labarin farashin da babban bankin kasar ba CBN ke saida kudin kasar Turai na EURO da kuma fan sterling na kasar Birtaniya. Ku na da labarin cewa farashin fetur na kara tsada ne a kasuwar Duniya wanda zai kawo sauki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel