Dandalin Kannywood: Mansura Isa tayi bikin murnar ranar haihuwar ta tare da nakasassu (Hotuna)

Dandalin Kannywood: Mansura Isa tayi bikin murnar ranar haihuwar ta tare da nakasassu (Hotuna)

Tsohuwar jarumar Kannywood wacce tauraronta ya haska a shekarun baya kuma uwargidan shahararren jarumi, Mansura Isa ta gudanar da bikin zagayowar ranar haihuwarta tare da nakasassu a jihar Kano.

A ranar Lahadi, 25 ga watan Fabrairu ne jarumar ta kara shekara a duniya, hakan yasa ta raya wannan rana tare da wadannan mutane.

Jarumar ta kuma nuna farin ciki da irin kaunar da yan uwa da abokan arziki suka nuna mata tare da sakonnin fatan alkhairi da suka aika mata.

Dandalin Kannywood: Mansura Isa tayi bikin murnar ranar haihuwar ta tare da nakasassu (Hotuna)
Dandalin Kannywood: Mansura Isa tayi bikin murnar ranar haihuwar ta tare da nakasassu

Mansura ta raya wannan rana mai matukar muhimmanci a rayuwarta tare da iyalenta da kuma abokan arzikin a zauren dake unguwar Nasarawa a jihar Kano.

Manyan jarumai da suka halarci wannan bikin domin taya ta murna sun hada da mai gidanta Sani Musa Danja, aminin mijinta Yakubu Muhammed, Mustapha Naburiska da babban mai shirya wasa Umar Gombe.

Dandalin Kannywood: Mansura Isa tayi bikin murnar ranar haihuwar ta tare da nakasassu (Hotuna)
Dandalin Kannywood: Mansura Isa tayi bikin murnar ranar haihuwar ta tare da nakasassu

KU KARANTA KUMA: Za mu gano kaf ‘Yan makarantar da aka sace a Yobe – Buhari

Mansura ta kyakkyawan samu yabo daga dimbin masoyanta inda suka jinjina mata bisa taimakon da take baiwa nakasassu mara galihu ta hanyar gidauniyar ta Todays life Foundation.

A baya Legit.ng ta kawo inda daya daga cikin sabbin fuskoki a masana'antar shirya fina-finan Hausa da ake yi wa lakani da Kannywood da ke da hedikwatar ta a garin Kano mai suna Halima Ibrahim ta siffanta masana'antar da wata makaranta dake cike da darussa da dama.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel