Yadda sakacin sojoji ya jawo kai harin makarantar sakandiren 'yan mata dake Dapchi - Gwamna Gaidam

Yadda sakacin sojoji ya jawo kai harin makarantar sakandiren 'yan mata dake Dapchi - Gwamna Gaidam

- Gwamnan jihar Yobe, Ibrahim Gaidam, ya dora laifin kai hari makarantar sakandiren 'yan mata dake Dapchi a jihar Yobe a kan sojin Najeriya

- A cewar Gaidam, da sojojin suna bakin aikin su da babu yadda za ai a kai harin balle har a sace daliban makarantar

- Gwamna Gaidam na wadannan kalamai ne yayin da ya karbi bakuncin gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, da ya kai masa ziyarar jaje

Gwamnan jihar Yobe, Ibrahim Gaidam, ya dora alhakin afkuwar harin da aka kai makarantar sakandiren 'yan mata dake Dapchi a kan sojojin dake jihar.

Gaidam ya bayyana cewar da sojojin na bakin aikin su babu yadda za ai a kai harin balle har a sace daliban makarantar, "mayakan kungiyar Boko Haram sun kawo harin ne sati daya bayan janye dakarun soji daga garin," a ceawar Gaidam.

Yadda sakacin sojoji ya jawo kai harin makarantar sakandiren'yan mata dake Dapchi - Gwamna Gaidam
Tawagar wakilcin gwamnatin tarayya yayin ziyarar Jihar Yobe a yau

Gwamnan na wadannan kalamai ne yayin da ya karbi bakuncin gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, wanda ya kai masa ziyarar jaje.

"Na dora alhakin faruwar wannan hari a kan sojoji da ma'aikatar tsaro da suka janye sojoji daga garin Dapchi. An kawo harin ne kasa da sati guda da janye dakarun soji daga garin. Kafin janye sojojin garin na zaune lafiya," a cewar gwamna Gaidam.

KARANTA WANNAN: Kullum mai dakina sai tayi kuka - Tsohon shugaban kasa Mugabe

Gaidam ya alakanta harin da irin abinda ya taba faruwa a makarantar sakandiren Buni Yadi a shekarar 2013, wanda ya ce ya faru ne sati daya kacal bayan janye sojoji daga garin.

Ana zargin cewar mayakan kungiyar Boko Haram sun sace dalibai mata daga makarantar sakandiren Dapchi a harin da suka kai ranar Litinin.

Gwamnatin tarayya ba ta fitar da alkaluman adadin 'yan matan da basu dawo makarantar ba ya zuwa yanzu.

Ministan yada labarai, Lai Mohammed, da takwaransa na harkokin cikin gida, Abdulrahman Dambazau, na can jihar Yobe domin tantance gaskiyar halin da ake ciki bayan kai harin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel