Kudirin daidaiton jinsi zai ruguza tarbiyar matasa da tsarin iyali - Mabiya darikar Katolika

Kudirin daidaiton jinsi zai ruguza tarbiyar matasa da tsarin iyali - Mabiya darikar Katolika

- Kungiyar bishof-bishof na Najeriya (CBCN) sunyi gargadin cewa kudirin daidaiton jinsi da aka gabatar gaban majalisa na iya ruguza tarbiyar al'umma da iyali

- CBCN kuma ta koka kan yadda ake rabawa matasa kwaroron roba da magungunan kare samuwar juna biyu a makarantu da wasu wuraren

- Kungiyar ta kuma shawarci gwamnatin tarayya ta mayar da hankali wajen samar da kayayakin rajistan zabe a duk sassan kasar nan

Kungiyar bishof-bishof mabiyar darikar katolika na Najeriya (CBCN) tayi korafi kan kudirin daidaita jinsi da aka gabatar gaban majalisar tarayya, a cewar kungiyar, kudirin sai bayar da damar barna iri-iri wanda suka sabawa rayuwan bil-adama ta na iyali.

Fastocin darikar katolika sun nuna kin amincewar su da kudirin daidaita jinsi
Fastocin darikar katolika sun nuna kin amincewar su da kudirin daidaita jinsi

Kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito, sanarwan da kungiyar ta bayar mai dauke da sa hannun tsohon shugaban kungiyar, Ignatius Kaigama a karshen taron su a Abuja, ta nuna rashin amincewar ta kan yadda ake rabawa dalibai kororon roba da kuma magungunan kare samuwar juna biyu.

KU KARANTA: EFCC zata waiwayi kwamitin zartarwa na APC karkashin jagorancin Odigie-Oyegun

"Duk da cewa mun amince akwai wasu hakokin mata da ya kamata a duba don yin gyara a kai, akwai wasu sassan kudirin na daidaiton jinsi da ba mu yarda da shi ba musamman sassan da zasu bayar da daman al'umma su rika aikata abubuwan da sukaci karo da rayuwa da kuma tarbiyyar iyali, muna kira da a ayi fatali da wadannan sassan.

"Bugu da kari, bamu amince da yadda ake rabar da kwaroron roba a makarantu, sansanin yan hidiman kasa da kuma asibitocin gwamnati da masu zaman kansu ba. Babu mahalukin da ke da ikon daukan ran wani." inji sanarwan

Malaman addinin kuma sunyi kira da gwamnati da mayar da hankali wajen samar da kayayakin rajistan zabe a dukkan sassan kasar nan. Sun kuma yi Allah wadai kan yadda kananan yara ke jefa kuri'a a jihar Kano.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel