Na mallaki Biliyoyi ga shi ban da ko Digiri a Duniya - Alakija

Na mallaki Biliyoyi ga shi ban da ko Digiri a Duniya - Alakija

- Folorunso Alakija ce wanda ta fi kowa dukiya a matan kasar nan

- Attajirar tace ita ba ta samu damar shiga Jami’a tayi karatu ba

- Asalin Iyayen ta Musulmai ne amma ita dai rikakkar kirista ce

Wannan karo mun kawo maku labarin wata Baiwar Allah da ta fi kusan kaf matan Duniya dukiya amma ba ta yi karatu a Jami’a ba. Folorunso Alakija yanzu tana da makudan Bilioyi a kasa.

Na mallaki Bilioyi ga shi ban da ko Digiri a Duniya - Alakija
Ta tara kudi a Duniya amma ba ta yi karatu a Jami’a ba

Matar da ta fi kowa kudi a kasar nan Folorunso Alakija ta bada labarin rayuwar ta a shafin Instagram inda tace ta tashi ita ce ta 8 a gidan su cikin yara sama da 50. A haka dai tayi ta fama da rayuwa har ta kai inda ta kai.

KU KARANTA: Gobara ta tashi a sansanin 'yan gudun hijira

Alakija ta bayyana cewa ita mata ce mai ibada da tsoron Ubangijin ta wanda wannan ya taimake ta. Iyayen Alakija mai shekaru 67 da haihuwa a Duniya dai Musulmai ne amma ita ta rungumi addinn Kirista da gaske.

Shekaru da dama da su ka wuce tace ta so ta zama Lauya amma Mahaifin ta bai bata dama ba. Yanzu dai wannan mata ta tada kai da Biliyoyi kuma ba ta taba samun damar zuwa Jami’a har ta samu shaidar Digiri ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel