Kasar Saudiyya zata saka kudi $64b, domin samar da wuraren shakatawa

Kasar Saudiyya zata saka kudi $64b, domin samar da wuraren shakatawa

- Kasar Saudiyya ta dauki kudurin bude wuraren shakatawa a fadin kasar

- Za'a gina wuraren casu domin nishadi ga al'ummar kasar da kuma baki

- Gwamnatin kasar ta bayyana kudurin ta na barin mata su dinga shiga wuraren shakatawa, ciki kuwa hadda basu izinin tuka motoci

Kasar Saudiyya zata saka kudi $64b, domin samar da wuraren shakatawa
Kasar Saudiyya zata saka kudi $64b, domin samar da wuraren shakatawa

Kasar Saudiyya ta ware kudi kimanin dala biliyan 64, domin bunkasa harkar shakatawa da nishadi, daga yanzu zuwa shekaru 10 masu zuwa.

Shugaban hukumar harkokin nishadi da shakatawa na kasar ya bayyana cewar an shirya wasanni kimanin 5,000 wanda za ayi a bana da suka kunshi wakokin cashewa na Maroon 5, kamar dai yanda kasar Amurka take yi.

DUBA WANNAN: An gurfanar da Al-Barnawi, shugaban 'Yan Ansaru, a gaban kotu a Abuja

A yanzu haka kasar Saudiyya din ta fara aiki da sauri-sauri na ginin wajen cashewar a birnin Riyadh dake kasar.

Kokarin saka jarin na daya daga cikin manufofin kasar na bunkasa tattalin arzikin a shekarar 2030, wanda Yarima Mohammed Bin Salman mai jiran gado ya gabatar shekaru biyu da suka wuce.

Yarima Mohammed Bin Salman yana son fito da wata sabuwar hanya da zata taimaka wurin bunkasa tattalin arzikin kasar na Saudiyya daban da dogaro da arzikin man fetir da suke yi a yanzu.

Kafofin yada labarai na kasar Saudiyya sun rawaito cewar, shugaban hukumar nishadi da shakatawa na kasar, Ahmed bin Aqeel al-khatib, ya na cewa, yana fatan wannan kokarin da suke zai taimaka wurin samun aikin mutane da yawa a kasar.

Wannan dai wani sabon al'amari ne a kasar ta Saudiyya, a kwanakin baya gwamnatin kasar ta bayyana cewar zata dinga kyale mata suna shiga filin kwallon kafa domin kallon wasanni, sannan kuma ta bayyana kudurin ta na kyale mata suyi tukin mota a kasar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel