Tattali arziki: Bankuna rututu sun fara ni-‘ya su daga tsarin CBN

Tattali arziki: Bankuna rututu sun fara ni-‘ya su daga tsarin CBN

- Bankuna da dama na cikin Najeriya ba su cika wasu sharudan CBN ba

- Babban bankin kasar nan ya gindaya wasu ka’idoji na tsarin hannun jari

- Yanzu haka wasu tsirarrun bankunan ne kurum su ka tsallake sharudan

Bankuna da dama na kasar nan za su gamu da babban cikas bayan da su ka gaza cika wani sabon sharadi da babban bankin kasar na CBN ya sa kwanan nan kamar yadda mu ka samu labari.

Tattali arziki: Bankuna rututu sun fara ni-‘ya su daga tsarin CBN
CBN sun sa Bankunan Najeriya da dama sun shiga halin uwar-bari

A farkon makon nan wata Ma’aikata ta Afrinvest da ke aiki a Yammacin Afrika ta bayyana cewa bankunan da za su sha a sabon tsarin da aka sa su ne Access Bank, Zenith Bank, Guaranty Trust Bank (GTB), First City Monument Bank (FCMB).

KU KARANTA: An sakawa FIRS harajin Tiriliyoyin kudi a bana

Sauran bankunan sun hada da Wema Bank da kuma United Bank for Africa Watau UBA. Wannan dai zai kawowa manyan bankunan kasar illa bankin Unity bank da kuma Union bank a wannan shekarar kamar yadda harsashen da aka yi ya nuna.

Irin su Diamond Bank, Fidelity Bank, Stanbic IBTC, Sterling da Union Bank za su shiga wani takunkumi a bisa wannan sabon ka’ida na babban bankin kasar watau CBN game da kudin da ake zubawa masu hannun jari a bankunan ‘yan kasuwan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel