Wasu matasa 2 da laifin garkuwa da mutane sun shiga hannu a jihar Kano

Wasu matasa 2 da laifin garkuwa da mutane sun shiga hannu a jihar Kano

Hukumar 'yan sanda ta jihar Kano, ta yi ram da wasu matasa biyu da laifin yin garkuwa da wani karamin yaro dan shekara hudu a unguwar Dorayi dake tantagwaryar birnin na Dabo.

Jaridar Daily Trust ta bayar da sunayen su kamar haka; Jabir Usman Sule da kuma Bashir Aminu mai inkiyar Karsan, inda suka nemi iyayen yaron da su biya fansa ta N2m.

Bashir tare da jabir
Bashir tare da jabir

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan matasa sun aika da wasika ga iyayen yaron ne da take nuna bukatar fansa ta wannan adadi na kudi, inda cikin taku da binciken hukumar 'yan sanda suka yi masu wani simame ba tare da sun farga ba.

KARANTA KUMA: Ba zamu bari jam'iyyar APC ta sukurkuce ba - Akande

Rahotanni da sanadin kakakin rundunar 'yan sanda na jihar, DSP Magaji Musa Majiya sun bayyana cewa, an cafke matasan ne a ranar 11 ga watan Fabrairu, kuma an yi nasarar gano yaron da aka yi garkuwa da shi ba tare da biyan taro ko sisi ba.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, mutane 4 sun shiga hannu da laifin kisan wani jigo na jam'iyyar PDP a jihar Ribas.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel