Tsautsayi baya wuce ranarsa: Wasu ýan mata Uku sun yi asarar rayukansu sakamakon kulle kansu a cikin wata mota

Tsautsayi baya wuce ranarsa: Wasu ýan mata Uku sun yi asarar rayukansu sakamakon kulle kansu a cikin wata mota

Rundunar Yansandan jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wasu yan mata kananan yara guda uku a unguwar sabon gari na jihar Kano bayan da suka garkame kawunansu a cikin wata mota.

Daily Trust ta ruwaito kaakakin rundunar Yansandan jihar, Magaji Musa Majiya yana cewa: “Wannan motar na ajiye ne tsawon shekara guda ba tare da an yi amfani da ita ba, sai yaran suka shiga cikinta, daga bisani kuma suka rufe kansu a ciki.

KU KARANTA: Darajan Naira: Babban bankin Najeriya ta antaya dala miliyan 210 cikin kasuwar canji

“Sai dai sun yi kokarin bude kofar amma suka kasa, a sakamakon haka ne guda uku daga cikinsu suka mutu saboda karancin iska da kuma zafi, amma an samu guda daya da ta sha da kyar, kuma tuni muka garzaya da ita zuwa Asibiti don samun kulawa. ” Inji shi.

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar Juma’ar da ta gabata, da misalin karfe 3 na yamma, sa’annan shekarunsu bai wuce biyu zuwa hudu ba.

Sai dai duk kokarin da majiyar ta yi na jin ta bakin mahafan yaran ya ci tura, amma rundunar ta tabbatar da fara gudanar da bincike don tabbatar da ummul aba’isun lamarin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar NAIJ.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Da dumi-dumi: Majalisa ta fasa dawowa daga hutu ranar 25 ga wata, ta saka sabuwar rana

Da dumi-dumi: Majalisa ta fasa dawowa daga hutu ranar 25 ga wata, ta saka sabuwar rana

Da duminsa: Majalisa ta kara daga ranar dawowa daga hutu
NAIJ.com
Mailfire view pixel