Wani ɗan sandan bogi ya shiga hannu yayin karbar rashawar N15, 000 a garin Abuja

Wani ɗan sandan bogi ya shiga hannu yayin karbar rashawar N15, 000 a garin Abuja

A ranar Talatar da ta gabata ne, hukumar 'yan sanda ta gurfanar da wani matashi mai shekaru 34, Prince Williams, a gaban kotun majistire da laifin yin basaja ta ma'aikacin dan sanda.

Ana zargin wannan matashi mazaunin unguwar Gwarinpa ta garin Abuja, da laifin yin shiga ta ma'aikata tare da karber cin hanci da rashawa.

Jami'in ɗan sanda

Jami'in ɗan sanda

Mista Kufreabasi Ebong, jami'in dan sanda mai shigar da kara ya shaidawa kotun cewa, wannan matashi ya aikata laifukan ne da misalin karfe 10.00 na safiyar ranar 11 ga watan Fabrairu.

Ebong yake cewa, wanda ake zargi yayi shiga irin ta ma'aikacin dan sanda kuma ya karbe lasisin tuki da naira 15, 000 mallakain wani mutum da azal ta afkawa.

KARANTA KUMA: Dandalin Kannywood: Hotunan tsohuwar jaruma Abida Muhammad da angonta

NAIJ.com da sanadin jaridar The Punch ta fahimci cewa, wannan laifuka sun sabawa sassa na 132 da kuma 292 na dokar kasa.

A yayin da kotu ba ta kama sa dumu-dumu da laifukan da ake tuhumar sa ba, alkalin kotun Mista Taribo Jim, ya daga sauraron karar zuwa ranar 21 ga watan Maris, ya kuma bayar da belin sa kan kudi N50, 000.

Jaridar NAIJ.com ta kuma ruwaito cewa, kasafin kudin 2018 ya tanadarwa wasu ma'aikatun kasar nan biyar N221m wajen kayartar da su a fannin ci da sha.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Da dumi-dumi: Majalisa ta fasa dawowa daga hutu ranar 25 ga wata, ta saka sabuwar rana

Da dumi-dumi: Majalisa ta fasa dawowa daga hutu ranar 25 ga wata, ta saka sabuwar rana

Da duminsa: Majalisa ta kara daga ranar dawowa daga hutu
NAIJ.com
Mailfire view pixel