Yan sanda sun kama mutane 2 da ake zargi da kisan dalibin ABU

Yan sanda sun kama mutane 2 da ake zargi da kisan dalibin ABU

Rundunar yan sanda reshen jihar Kaduna tace ta kama wadansu mutane biyu dake da hannu a kisan wani dalibi a jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria.

“Mun kama mutane biyu da ake zargi da hannu a kisan dalibin ABU; an kama daya a ranar Lahadi yayinda aka kama dayan a ranar Litinin,” kakakin rundunar, Muktar Aliyu ya fada ma kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a ranar Talata, 20 ga watan Fabarairu a Kaduna.

Yace masu laifin na amsa tambayoyi sannan za a mikasu zuwa kotu bayan an kammala bincike.

Yan sanda sun kama mutane 2 da ake zargi da kisan dalibin ABU

Yan sanda sun kama mutane 2 da ake zargi da kisan dalibin ABU

KU KARANTA KUMA: Hukumar SUBEB ta hana wazifa a makarantun Tsangayar

NAN ta ruwaito cewa an kashe marigayin wanda ya kasance dalibin karatun likitan dabbobi a ranar Juma’a.

A wani lamari na daban NAIJ.com ta samu labari cewa a halin yanzu Jam’iyyar APC ta shiga halin ba-kan-ta a Jihar Kogi inda har ta kai Gwamnan Jihar ya nada wasu sababbin Shugabannin Jam’iyyar a Jihar a makon da ya wuce.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Tsoho ya yiwa wata mata wanka da ruwan acid, kalli hoton

Tsoho ya yiwa wata mata wanka da ruwan acid, kalli hoton

Tsoho ya yiwa wata mata wanka da ruwan acid, kalli hoton
NAIJ.com
Mailfire view pixel