Majalisar dattawa tayi Allah wadai da rushe sakatariyar APC da El-Rufai yayi

Majalisar dattawa tayi Allah wadai da rushe sakatariyar APC da El-Rufai yayi

Majalisar dattawa tayi Allah wadai da rushe sakatariyar sashen jam’iyyar APC a jihar Kaduna.

NAIJ.com ta rahoto cewa gwamnatin jihar Kaduna ta rushe ofishin bangaren jam’iyyar APC da ta dakatar da gwamna Nasir El-Rufai a ranar Talata, 20 ga watan Fabarairu.

Da yake Magana a zauren majalisa a ranar Talata, 20 ga watan Fabrairu, dan majalisa mai wakiltan Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Shehu Sani, ya bayyana cewa El-Rufai da kansa ya yi jagoranci tare da kula da rushe ofishin sashen jam’iyyar APC din.

Majalisar dattawa tayi Allah wadai da rushe sakatariyar APC da Rl-Rufai yayi

Majalisar dattawa tayi Allah wadai da rushe sakatariyar APC da Rl-Rufai yayi

A nashi bangaren, mataim akin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu yace baza a taba cimma mulkin damokradiyya ba a karkashin irin wannan danniyan da tauye hakki ba.

KU KARANTA KUMA: Zamu marawa Buhari baya idan ya sake takara a 2019 – Dattawan kudu maso gabas

Kamar yadda muka kawo maku a baya Gwamnatin jihar Kaduna ta rusa Hedkwatar sashin jam’iyyar APC da ta dakatar da gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, har na tsawon watanni shida.

NAIJ.com ta samu rahoton cewa, an rusa ofishin ne dake gida mai lamba 11B, Sambo road, GRA Kaduna,da kariyan jami’an tsaro da misalin karfe 4 na safiyan ranar Talata.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Tsoho ya yiwa wata mata wanka da ruwan acid, kalli hoton

Tsoho ya yiwa wata mata wanka da ruwan acid, kalli hoton

Tsoho ya yiwa wata mata wanka da ruwan acid, kalli hoton
NAIJ.com
Mailfire view pixel