An yankewa wani dalibi mai shekaru 18 da ya sace babur daurin shekara daya

An yankewa wani dalibi mai shekaru 18 da ya sace babur daurin shekara daya

- Wani matashin dalibi mai shekaru 18 ya sace babur na kimanin kudi N120,000 a Jos

- Ya amsa laifin da a ka tuhume sa da shi yayin da ya shiga hannun Hukuma

- Kotu ta yanke ma sa daurin shekara 1 ko biyyan tara na N10,000

Wata kotu da ke Kasuwan Nama a garin Jos na Jihar Pilato, ta yankewa wani matashin dalibi mai shekaru 18, gidan wakafi na shekara 1. Dalibin mai suna Mustapha Ruwanu, ya sace babur ne na kimanin kudi N120,000.

An yankewa wani dalibi mai shekaru 18 da ya sace babur daurin shekara 1
An yankewa wani dalibi mai shekaru 18 da ya sace babur daurin shekara 1

Alkalin Kotun, Mista Yahaya Mohammed, ya yankewa Ruwanu hukuncin daurin shekara 1 ko kuma biyan tara na N10,000 bayan ya amsa laifin da a ke tuhumar sa da shi.

KU KARANTA: FAAN ta dakatar da shugaban tsaro na filin jirgi kan sakaci da ya yi shanu suka mamaye titin jirgi

Jami'in Hukumar 'Yansanda wanda ya gurfanar da mai laifin gaban kotu, Sajen Ibrahim Gokwat, ya bayyana cewar wani mai suna Abubakar Hassan na Mista Ali, shi ne ya shigar da karar a ranar 20 ga watan Disamba na 2017 a ofishin 'yansanda da ke Anguwan Rogo.

Hassan ya bayyana cewar ya dauki Ruwanu ne a kan babur din a ranar zuwa ASD Plaza, inda a nan ne Ruwanu ya kawo shawarar su je su yi sallah a masallaci. Su na cikin masallacin ne sai shi Ruwanu ya fito ya tsere da mashin din.

Gokwat ya bayyana cewar wanda a ke zargi ya amsa laifin sa yayin da ya shiga hannun kuma. Ya kara da cewar laifin ya sabawa sashi na 287 na dokar da'a ta final kod na Arewacin Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel