An kama masu sibaren-na-baiye a jihar Legas ta hanyar amfani da na'urorin tsegumi

An kama masu sibaren-na-baiye a jihar Legas ta hanyar amfani da na'urorin tsegumi

- Wani faifan bidiyo da na'urorin tsegumi na gefen hanya a jihar Legas suka nada sun tona asirin wasu batagari

- An kama masu sibaren aljihun mutane daban-daban ta hanyar amfani da na'urorin da aka saka domin inganta tsaro a garin Legas

- Kakakin hukumar 'yan sanda a jihar Legas, SP Chike Oti, ya ce nan bada dadewa ba za'a gurfanar da wadanda aka kama din gaban kotu

Wani faifan bidiyo da na'urorin tsegumi na gefen hanya suka hada a garin Legas sun tona asirin wasu batagari dake sibaren aljihun jama'a.

Na'urorin tsegumi guda uku ne suka tona asirin batagarin yayin da suke aikata mugun halinsu.

Gwamnatin jihar Legas ce ta dasa na'urorin a manyan titunan jihar domin saukakawa jami'an 'yan sanda masu aikin ko-ta-kwana (RRS) hanyoyin gano duk inda ake aikata laifi ko batagari ke boyewa.

An kama masu sibaren-na-baiye a jihar Legas ta hanyar amfani da na'urorin tsegumi
Na'urar tsegumi

Wadanda jami'an RRS su ka yi nasarar cafke wa ta hanyar bin sahun su bayan aikata sane ga jama'a sun hada da; Jelili Ganiu; mai shekaru 19, Samson Owolabi; mai shekaru 23, Segun Lawoye; mai shekaru 47, da kuma Toyin Samuel; mai shekaru 38. An kama su ne a ranakun Alhamis da Juma'a.

Wata majiyar hukumar 'yan sanda ta sanar da cewar an kama masu laifin ne a karkashin gadar Oshodi inda suke aikata laifin kuma daga nan ne jami'an RRS suka bi sahun su tare da damko su.

DUBA WANNAN: Labari da duminsa: Shugaba Buhari ya ja kunnen magu, ya bashi wa'adin kwana hudu ya kare kansa

Kazalika hukumar 'yan sanda ta sanar da kama wasu mutane biyu; Latoye da Samuel, mata da miji, dake aikata laifin sane ga jama'a kuma hukumar ta nuna masu faifan bidiyonsu yayin da suke tsaka da tafka sata.

Kakakin hukumar 'yan sanda a jihar Legas, SP Chike Oti, ya ce zasu gurfanar da wadanda aka kama gaban kotu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel