Makiyaya suna ci gaba da kai mana hari a jihar Benue - Gwamna Samuel Ortom

Makiyaya suna ci gaba da kai mana hari a jihar Benue - Gwamna Samuel Ortom

- Gwamna jihar Bneuwe ya ce har yanzu mutane jihar sa suna fuskanta barazanar hare-hare daga makiyaya

- Samuel Ortom ya ce hadda jami'an tsaro basu tsira daga hare-haren makiyaya ba a jihar Benuwe

Gwamnan jihar Beuwe, Samuel Ortom dake yankin Arewa ta tsakiya ya ce har yanzu mutanen jihar sa, suna cigaba da fuksantar haren-haren daga makiyaya.

Gwamna Samuel Ortom, ya bayyana hake ne a zantawar da yayi da manema labaru a ranar Lahadi a brinin Makurdi.

Makiyaya sun ci gaba da kai mana hari a jihar Benue - Gwamna Samuel Ortom
Makiyaya sun ci gaba da kai mana hari a jihar Benue - Gwamna Samuel Ortom

Gwamnan ya kara da cewa “babban damuwar shi akan al’amarin shine jami’an tsaro kan su ba su tsira daga wadannan mahara ba.

KU KARANTA : An kusa kashe ni saboda na ki barin kananan yara su kada zabe – Tsohon kwamishinan INEC

"Jami’an ‘yan sanda sun nuna gazawarsu, kuma har yanzu sojojin da ake zance ba su fara aiki ba.”

Alkaluman kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International na cewa akalla mutane 168 ne suka rasa rayukansu a jihar daga watan janairu zuwa yau.

Idan aka tuna baya Legit.ng ta rawaito labarin attisayen gudun muzuru da rundunar sojojin Najeriya ta kaddamar a yankin Arewa ta tsakiya a makon da ta gabata dan kawo karshen matsalolin da yankin ke fuskanta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel