Yan hana ruwa gudu ke haddasa rashin man fetur a Najeriya – Kwamitin majalisar wakilai

Yan hana ruwa gudu ke haddasa rashin man fetur a Najeriya – Kwamitin majalisar wakilai

- An zargi yan hana ruwa gudu da haddasa karancin man fetur da ake fama da shi a fadin Najeriya

- Kwamitin binciken ayyukan ma’aikatan NPMC na majalisar wakilai ne ta bayyana hakan

- Shugaban kwamitin, Danlami Kurfi, ya bayyana cewa wadannan mutane suna buwayar kokarin gwamnatin tarayya

Majalisar wakilai ta zargi yan hana ruwa gudu da haddasa karancin man fetur a fadin kasar.

Kwamitin binciken ayyukan ma’aikatan NPMC na majalisar wakilai ne ta bayyana hakan a ranar Alhamis, 15 ga watan Fabrairu.

A lokacin da ya kai wani ziyara matatar Port Harcourt, shugaban kwamitin, Danlami Kurfi ya ce wadannan yan hana ruwa sune suka hadda karancin man fetur da ake fuskanta a kasar.

Yan hana ruwa gudu ke haddasa rashin man fetur a Najeriya – Kwamitin majalisar wakilai

Yan hana ruwa gudu ke haddasa rashin man fetur a Najeriya – Kwamitin majalisar wakilai

Kurfi wanda ya kasance dan majalisa mai wakiltan Dutsin-ma/Kurfi na jihar Katsina, yace binciken da kwamitin tayi zuwa yanzu ya nuna cewa gwamnati a bangarenta ta NNPC tana samar da lokaci domin shawo kan matsalar.

KU KARANTA KUMA: Hadimin gwamnan jihar Katsina ya kashe yarsa da mota

Dan majalisar ya bayyana cewa wasu ne ke buwayar kokarin da gwamnati ke yi.

A baya NAIJ.com ta rahoto cewa Alhaji Sule Lamido, tsohon gwamnan jihar Jigawa sannan kuma dan takarar shugabancin kasa a jam'iyyar PDP yayinda yake tarban sama da mutane 5,000 da suka sauya sheka daga APC zuwa PDP ya sha alwashin kayar da shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019 idan har jam'iyyarsa ta basa tikitin takarar shugabancin kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Tsoho ya yiwa wata mata wanka da ruwan acid, kalli hoton

Tsoho ya yiwa wata mata wanka da ruwan acid, kalli hoton

Tsoho ya yiwa wata mata wanka da ruwan acid, kalli hoton
NAIJ.com
Mailfire view pixel