Kisa a jihar Zamfara: 'Yan sandan Najeriya sun kama mutane 3

Kisa a jihar Zamfara: 'Yan sandan Najeriya sun kama mutane 3

Jami'an tsaro na hukumar 'yan sandan Nijeria ta bayyana cewa ta samu nasarar kama akalla wasu mutane uku da take zargin su da hannu dumu-dumu a kashe-kashen da suka auku a baya-baya nan da aka yi a jihar Zamfara dake a arewa maso yammacin kasar nan.

Yan sandan dai a cikin wata sanarwa da ke dauke da sa hannun kakakin hukumar, CSP Jimoh Moshood ya bayyana cewa mutanen da suka cafke haka zalika suna bada hadin kai a bincike da 'yan sanda suke yi.

Kisa a jihar Zamfara: 'Yan sandan Najeriya sun kama mutane 3

Kisa a jihar Zamfara: 'Yan sandan Najeriya sun kama mutane 3

KU KARANTA: Makiyaya sun kashe zakuna 3

NAIJ.com ta samu haka zalika cewa sanarwar ta cigaba da bayyana cewa da zarar hukumar ta 'yan sandan sun kamala binciken da su ke yi , za a gurfanar da mutanen a gaban kotu.

Wadanda ake zargin dai sun hada Halilu Garba mai shekara 45 da Zubairu Marafa mai shekara 45 da kuma Nafi'u Badamasi mai shekara 40.

A wani labarin kuma, Sarkin Maradun na jihar Zamfara mai suna Alhaji Garba Tambari ya kwarmatawa 'yan jarida cewar tuni shi da wasu sauran sarakunan gargajiya a dukkan fadin kasar nan sun yanke shawarar goyawa shugaba Muhammadu Buhari baya a zaben shekarar 2019.

Sarkin na Maradun yayi wannan ikirari ne a yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan da gama ganawa da shugaban da a halin yanzu yake wata ziyara a garin sa na Daura dake a jihar Katasin.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain NAIJ.com HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duba hotuna: Dalibin Najeriya ya kera mota, ya fara zuwa makaranta a cikinta

Dalibin Najeriya ya fara zuwa makaranta a motar da ya kera, hotuna

Dalibin Najeriya ya fara zuwa makaranta a motar da ya kera, hotuna
NAIJ.com
Mailfire view pixel