JAMB ta kara bankado wani cuwacuwa na N86m a Jihohi 5

JAMB ta kara bankado wani cuwacuwa na N86m a Jihohi 5

- JAMB ta na zargin Ofisoshin ta na Jihohi 5 da karkatar da kudi na Jimillar N86m

- Jihohin sun hada da Edo da Kano da Kogi da Gombe sai kuma Jihar Filato

- An dakatar da jami'an da a ke zargi yayin da a ke gudanar da bincike

Cibiyar Shirya Jarabawar Shiga Makarantun Gaba da Sakandare (JAMB), ta bankado sabbin cuwacuwa na kudaden Cibiyar da a ka tafka na Jimillar N86 miliyan a Ofisoshin ta na Jihohin Edo da Gombe da Kano da Kogi kuma Jihar Pilato.

JAMB ta kara bankado wani cuwacuwa na N86 miliyan a Jihohi 5
JAMB ta kara bankado wani cuwacuwa na N86 miliyan a Jihohi 5

Jaridar Saturday Punch ta bayar da rahoton cewa kwamitin Bincike na Cibiyar ta na zargin Jihar Edo da karkatar da N31m, Kano N20m, Kogi kuma N7m, Kano N20m, Gombe N10m, sai kuma Pilato N15m.

KU KARANTA: APC na Jihar Kaduna ta dakatar da Hunkuyi, ta kuma kori wadansu 28

Mai magana da yawun JAMB, Dakta Fabian Benjamin, shi ne ya tabbatarwa manema labarai adadin kudin. Ya kuma ce Cibiyar ba za sa ido sosai wurin bincike, ba kuma za ta yarda da irin wanann cuwacuwa ba.

Wani jami'in JAMB da ya nemi a sakaya sunan sa ya shaidawa cewar an dakatar da jami'an da a ke zargi da tafka wannan cuwacuwa yayin da bincike ke gudana.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel