Zaben 2019: Maganar 'yan matan amarya Babangida da Obasanjo suke yi wa Buhari - Balarabe Musa

Zaben 2019: Maganar 'yan matan amarya Babangida da Obasanjo suke yi wa Buhari - Balarabe Musa

- Maganar 'yan matan amarya Babangida da Obasanjo suke yi wa Buhari - Balarabe Musa

- Ya bayyana cewa ko kusa ba maganar hankali bace tsaffin shugabannin kasar su ce wai Buhari kai ya nemi tazarce

- Yace cikin duka tsaffin shugabannin babu wanda ma ya kwatanta abun da shugaba Buhari ke yi

Tsohon gwamnan jihar Kaduna dake a Arewa maso yammacin kasar nan mai suna Alhaji Balarabe Musa ya yi kakkausan lafuzza ga tsaffin shugabannin kasar Najeriya Ibrahim Badamasi Babangida da kuma Cif Olusegun Obasanjo game da kamalamn su kan shugaba Muhammadu Buhari.

Zaben 2019: Maganar 'yan matan amarya Babangida da Obasanjo suke yi wa Buhari - Balarabe Musa
Zaben 2019: Maganar 'yan matan amarya Babangida da Obasanjo suke yi wa Buhari - Balarabe Musa

KU KARANTA: Yan bindiga sun kashe dan sanda a Kwara

Tsohon gwamnan, Alhaji Balarabe Musa ya bayyana cewa ko kusa ba maganar hankali bace tsaffin shugabannin kasar su ce wai kar shugaba Muhammadu Buhari ya sake tsayawa takarar tazarce a 2019.

Legit.ng ta samu cewa haka zalika ya bayyana cewa a cikin duka tsaffin shugabannin kasar ai babu wanda ma ya kwatanta abun da shugaba Buhari din ke yi a halin yanzu don haka kamata yayi su ja bakin su su yi shiru.

A wani labarin kuma, Tsohon shugaban kasar Najeriya na farko a wannan jamhuriyar Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa yana da yakinin cewa kasar Najeriya zata cigaba sosai shi yasa ma yake a raye da tuni ya bi ta wata hanyar ya kashe kan sa.

Haka zalika tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa babu wani mahalukin da ya isa ya hana shi fadar albarkacin bakin sa game da yadda lamurran kasar ke tafiya a ko yaushe indai har yana numfashi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel