Za'a nuna fim din littafin Tafawa Balewa a gasar bana ta fim a Berlin din kasar Jamus

Za'a nuna fim din littafin Tafawa Balewa a gasar bana ta fim a Berlin din kasar Jamus

- An buga Littafin Shaihu Umar ne a 1956, inda kuma aka wallafa shi a 1971

- Littafin yana nuna yadda aka yi bautarwa a zamanin da

- Yanzu za'a nuna ffim dinsa a kasar Jamus

Za'a nuna fim din littafin Tafawa Balewa a gasar bana ta fim a Berlin din kasar Jamus
Za'a nuna fim din littafin Tafawa Balewa a gasar bana ta fim a Berlin din kasar Jamus

Tsohon Firai-Minista na farko a Najeriya, Alhaji Tafawa Balewa, a gasar littattafai na adabin Hausa, ya taba rattaba wani littafi mai suna Shehu Umar, cikin littattafai da ya wallafa a zamaninsa, yanzu dai anyi fim dinsa za-kuma a gwada a sinimomi a kasar Jamus.

Littafin Shaihu Umar dai, labari ne mai ban tausayi, wanda aka wallafa, kagagge, na wani yaro da aka kama a zamanin bautar da bayi, aka sayar dashi, mahaifiyarsa ta tafi nemansa, ta samo shi bayan ya zaga duniya da hamada.

DUBA WANNAN: Budaddiyar wasika zuwa ga shugaba Buhari

Littafin na nuna yadda rayuwar mutan da take, ta soyayya da kawaici, da kuma tsaro na samamen barada masu kama bayi a yankunan tsakiyar Najeriya, domin bautarwa.

A yanzu dai an yi littafin, kuma za'a nuna shi a kasar Jamus a babban bikin baje kolin fina-finan na kasa da kasa na Berlin wadda zai gudana a kasar Jamus.

Manajan Darakta na hukumar fina-finai ta Nijeriya NFC, Chidia Maduekwe, shi ne ya bayyana hakan a ranar Litini, a yayin hirarsa da kamfanin dillancin labarai ta Nijeriya a Abuja. Ya ce, “Shehu Umar” wani labari ne kan bautar Afirka, wadda aka rubuta tun a 1966, inda kuma aka wallafa shi a shekara ta 1971, sannan kuma daga bisani a shekara ta 1976 aka dawo da littafin zuwa fim, wadda Adamu Halilu ya yi, wadda kuma Manajin Darakta na hukumar shirya fina-finai ta Nijieriya ya jagoranta.

Ya bayyana cewar, yanzu haka sun kammala dukkanin shirye-shiryen nuna wannan fim din a babban taron kasa da kasa na shekara-shekara na da ake yi a Berlin, taron baje fim din wadda zai gudana a watan Fabrairu a ranakun 15 zuwa 25.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel