Akalla mutane 1,400 ne aka kashe a Zamfara cikin shekara 5 - Sanata Marafa

Akalla mutane 1,400 ne aka kashe a Zamfara cikin shekara 5 - Sanata Marafa

- Akalla mutane 1,400 ne aka kashe a Zamfara cikin shekara 5 - Sanata Marafa

- Sanatan yayi wannan ikirarin ne a yayin da yake zantawa da wakilin majiyar mu

- Kwamishin kananan hukumomin jihar ya ce kalaman dan majalisar ya yi na cike da kura kurai

Kamar dai yadda muke samu daga majiyar mu, Sanata Kabiru Marafa, mamba a majalisar dattijan tarayyar Najeriya dake wakiltar mazabar jihar Zamfara ya yi ikirarin cewa yan bindiga sun kashe akalla mutane 1,400 a jihar a cikin shekaru 5 kacal da suka gabata.

Akalla mutane 1,400 ne aka kashe a Zamfara cikin shekara 5 - Sanata Marafa
Akalla mutane 1,400 ne aka kashe a Zamfara cikin shekara 5 - Sanata Marafa

KU KARANTA: Ba mu san inda Shekau yake ba - Sojin Najeriya

Sanatan yayi wannan ikirarin ne a yayin da yake zantawa da wakilin majiyar ta mu inda ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar ta gaza sosai wajen kariya ga dukiya da kuma rayukan al'ummar ta.

Legit.ng ta samu cewa sai dai kwamishin kananan hukumomin jihar mai suna Alhaji Bello Dankande, ya gaya wa majiyar ta mu cewa kalaman dan majalisar ya yi na cike da kura kurai.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a cikin makon jiya ma dai an ruwaito cewa wasu da ake kyautata zaton barayin shanu ne sun kashe mutane da dama a karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara din.

Hukumomi sun ce suna daukar matakai kan batun, amma masu sharhi kan sha'anin tsaro da ma 'yan kasar na ganin matakan da ake dauka ba su yi tasirin hana kai hare-haren ba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel