'Yan Najeriya sun koka da sabon tsarin samun izinin shiga kasar Saudiyya

'Yan Najeriya sun koka da sabon tsarin samun izinin shiga kasar Saudiyya

- 'Yan Najeriya sun koka kan sabuwar dokar tantance matafiya kasar Saudiyya ta hanyar daukan bayannan su a na'urar komfuyuta

- A duk fadin Najeriya, wurare uku kawai aka ware don gudanar da tantancewar kuma hakan ya haifar da cinkoso da wasu wahalhalu ga matafiya

- Kungiyar masu kula masu zuwa aikin Hajj da Umarah (AHOUN), itama ta koka kan yadda kamfanin da aka bawa kwangilar tantance matafiyar ke gudanar da aikin

Maniyata 'yan Najeriya da ke son zuwa Kasar Saudiyya don sauke farali sun koka kan wahalwalun da ke tatare da sabuwar hanyar daukan bayanan matafiya ta hanyar na'aurar mai kwakwalwa da kasar ta bullo da shi.

'Yan Najeriya son koka da sabon tsarin samun izinin shiga kasar Saudiyya
'Yan Najeriya son koka da sabon tsarin samun izinin shiga kasar Saudiyya

A dai shekara 2017 ne mahukuntar kasar na Saudiyya sukayi garambawul da dokokin kasar inda suka wajabta daukan bayanan maniyyata ta hanyar na'urar mai kwakwalwa.

KU KARANTA: NNPC ta samar da lita miliyan 29.058 na fetir ga jihohi 13 a Arewa cikin kwanaki uku

Bugu da kari, a duk fadin Najeriya wurare uku kawai a ka ware don yin rajistar a Abuja, Kano da kuma Legas. Hakan ya sa ake samun cinkoso da wahalwalu wajen yin rajistan.

Maniyata da suka zanta da jaridar Daily Trust a ofishin wata kamfani mai suna VFS Tasheel wadda kasar Saudiyya ta bawa kwangilan tantance masu son tafiya kasar ta Saudiyya sun koka kan yadda suka dade a ofishin kafin a tantance su.

Wata mai son tafiya kasar Saudiyyar daga Maiduguri da ta nemi a sakaya sunan ta ta ce "Nayi tsamanin za'a yi min rajistan cikin yan sa'o'i kadan amma na kwashe kwanaki ina zuwa."

Itama Kungiyar masu kula da matafiya Hajji da Umarah na Najeriya (AHOUN) ta nuna damuwar ta kan yadda kamfanin da aka bawa kwangilar tantance matafiyar ke kawo tangarda ga yan Najeriya.

Mataimakin shugaban Kungiyar, Tijjani Uba Waru, ya fadawa Daily Trust cewa rashin gagawa wajen tantance matifyan na janyo wa matafiya asarar dimbin miliyoyin naira.

Duk kokarin da akayi don ji ta bakin jami'an kamfanin na VFS Tasheel ya ci tura.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel