Hukumar 'Yansanda ta kama kungiyar ma su garkuwa da mutane da satar shanu

Hukumar 'Yansanda ta kama kungiyar ma su garkuwa da mutane da satar shanu

- Hukumar 'Yansanda na Jihar Kwara ta kama Kungiyar 'yan fashi da garkuwa da mutane

- Ta samu nasarar dawo da shanaye 233 da su ka sace su ka tafi da su Jihar Neja

- Ta kuma kama 'yan fashin babur a Ilori tare da dawo da babura 10 da su ka sace

Hukumar 'Yansanda na Jihar kwara ta kama kungiyar 'yan fashi da garkuwa da mutane da su ka yi awon gaba da shanaye sama da 200. Kwamishinan 'Yan sanda na Jihar, Lawan Ado, shi ne ya bayyana hakan yayin nunawa manema labarai bayani kan fashin.

Hukumar 'Yansanda ta kama kungiyar ma su garkuwa da mutane da barayin shanu
Hukumar 'Yansanda ta kama kungiyar ma su garkuwa da mutane da barayin shanu

Ado ya ce jami'an sa sun samu nasarar kama 'yan fashin ne da hadin gwiwan jami'an 'yansanda na Makwa ta Jihar Neja, inda can ne 'yan fashin su ka tsere. Sai dai kuma jami'in Hukumar Yaki da Fashi ta SARS mai Machi Yusuf, ya rasa ran sa.

DUBA WANNAN: Ziyarar da muka kaiwa Buhari bata da nasaba da zaben 2019, Inji Gwamnonin APC

Yusuf ya rasa ran sa ne yayi musayen wuta da shugaban 'yan fashin mai suna Adamu Abacha. Abacha ya fece cikin daji inda nan ne jami'an SARS din su ka tsinci gawar sa da bindiga kirar AK47 da ya binne.

Kwamishinan ya bayyana cewar an samu dawo da shanaye 233. An kuma kwace alburusai 6 baya ga bindigar da a ka kwace. Za kuma a gurfanar da 'yan fashin 6 a kotu idan a ka kammala bincike.

Kwamishinan ya kuma bayyana cewar an kama wasu masu garkuwa da mutane guda 4, da su ka sace wani Hassan Taiye a masallacin sa da ke Chikanda da ke Karamar Hukumar Baruten na Jihar. An kuma kama wasu 'yan fashin mashin a Ilorin da babura 10.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel