Don magance tsaro: Gwamnatin tarayya za ta samar wa matasa 300,000 aiki

Don magance tsaro: Gwamnatin tarayya za ta samar wa matasa 300,000 aiki

Ministan labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta shirya tsaf domin samar wa matasa 300, 000 sabbin aikin yi a shekarar nan ta 2018 domin kare su daga afkawa ta'addanci dake yiwa tsaro barazana.

Ministan yake cewa, gwamnatin za ta tanadi wannan ayyuka ne karkashin shirin nan na N-Power da take ci gaba da gudanarwa.

Ministan labarai da al'adu; Alhaji Lai Mohammed

Ministan labarai da al'adu; Alhaji Lai Mohammed

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, ministan ya bayyana hakan ne a yayin gabatar da jawabai a wurin taro kan tsare-tsare na kasa dangane da hanyoyi na kawar da ta'addanci da kawo karshen sa a kasar nan.

KARANTA KUMA: Cututtuka 8 da ka iya shafe duniya cikin kiftawar idanu

Lai Mohammed ya kara da cewa, yanayi na rashin aiki, talauci, rashin ilimi da kuma cin hanci da rashawa suke bai wa matasa karfin gwiwa na fadawa ta'addanci, inda yake cewa gwamnatin za ta dauki matasa 300, 000 aiki doriya kan 200, 000 dake aikin karkashin shirin ta N-Power.

Jaridar NAIJ.com ta kuma ruwaito cewa, ma'aikaciyar nan ta JAMB ta ƙaryata rahoton N36m da maciji ya hadidiye a ofishin su dake birnin Makurdi a jihar Benuwe.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abinda yasa dole Saraki zai yi murabus daga kujerarsa - Gbajabiamila

Abinda yasa dole Saraki zai yi murabus daga kujerarsa - Gbajabiamila

Dalilin da yasa dole Saraki zai yi murabus daga kujerarsa - Gbajabiamila
NAIJ.com
Mailfire view pixel