Gwamnatin tarayya ta roki Dangote ya taimaketa ya kammala matatar man sa kafin 2019

Gwamnatin tarayya ta roki Dangote ya taimaketa ya kammala matatar man sa kafin 2019

- Gwamnatin tarayya ta roki Dangote ya taimaketa ya kammala matatar man sa kafin 2019

- Karamin ministan albarkatun man fetur Mista Ibe Kachikwu ne ya bayyana hakan

- Ya kuma tabbatar wa da shahararren dan kasuwar cikakken goyon bayan gwamnatin ta su gare shi

Gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta roki shahararren mai kudin nan Alhaji Aliko Dangote da ya taimaketa ya karasa matatar man sa kafin zaben 2019.

Gwamnatin tarayya ta roki Dangote ya taimaketa ya kammala matatar man sa kafin 2019

Gwamnatin tarayya ta roki Dangote ya taimaketa ya kammala matatar man sa kafin 2019

KU KARANTA: Za'a ba Aisha Buhari kyautar girmamawa

Gwamnatin tarayyar tayi wannan kiran ne a ta bakin karamin ministan albarkatun man fetur Mista Ibe Kachikwu wanda ya ziyarci inda ake gina matatar man a garin Legas.

NAIJ.com ta samu labarin cewa minista Mista Ibe Kachikwu ya ce gwamnatin shugaba Buhari ta dogara kacokan ne akan dan kasuwar musamman wajen cika alkawuran da ta daukar wa yan Najeriya na barin shigowa da tattaccen mai daga kasashen waje.

Ministan kuma har ila yau ta tabbatar wa da shahararren dan kasuwar cikakken goyon bayan gwamnatin ta su gare shi don ganin an kammala matatar man kuma ta fara aiki kafin zaben.

A wani labarin kuma, Hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake da alhakin kayyade farashin man fetur a gidan man kasar nan watau Department of Petroleum Resources, DPR ta sanar da samun nasarar kunlle akalla gidajen mai 15 a jihar Akwa ibom dake a kudu maso kudancin kasar nan.

Hukumar dai ta bayyana cewa ta kulle gidajen man ne saboda sabawa umurnin kasa na saida mai a kan farashin da ya haura ma Naira 145 a jihar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain NAIJ.com HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dalilin da yasa dole Saraki zai yi murabus daga kujerarsa - Gbajabiamila

Dalilin da yasa dole Saraki zai yi murabus daga kujerarsa - Gbajabiamila

Dalilin da yasa dole Saraki zai yi murabus daga kujerarsa - Gbajabiamila
NAIJ.com
Mailfire view pixel