An samu babbar baraka a cikin Jam’iyyar APC mai mulki

An samu babbar baraka a cikin Jam’iyyar APC mai mulki

- Jam’iyyar APC ta samu baraka yayin da ake shirin zaben 2019

- Akwai wadanda ke tare da Majalisa da wasu tsofaffin Gwamnoni

- Yanzu dai an nada Bola Tinubu ya shawo kan karshen duk rikicin

Mun samu rahoto daga Jaridar Daily Trust cewa an samu baraka a cikin Jam’iyyar APC mai mulki inda har aka raba Jam’iyyar gida 4. Yanzu haka dai an dauki mataki na shawo kan karshen rikicin wanda wasu ke ganin da kamar wuya.

An samu babbar baraka a cikin Jam’iyyar APC mai mulki

An samu babbar baraka a cikin Jam’iyyar APC mai mulki

Kwanan nan Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Bola Tinubu ya sasanta rikicin cikin gidan da ke Jam’iyyar APC. Sai dai wasu na ganin cewa Bola Tinubu na daga cikin wadannan matsaloli kuma zai yi wahala ayi nasara.

KU KARANTA: Gwamnan APC na neman tsaida surukin sa takara

Daga cikin bangarorin da aka samu akwai na ‘Yan Majalisa wanda ke dauke da wasu tsofaffin Gwamnonin Kasar. Tun bayan nada Shugabannin Majalisa dai aka ja layi da Jam’iyyar APC da ma irin su Jigon Jam’iyyar Bola Tinubu.

Bayan nan kuma akwai bangaren Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai da kuma Ministan Sufuri Rotimi Amaechi. Sannan kuma akwai wadanda su ke tare da Shugaban Kasa Buhari. Haka kuma akwai barin da ke tare da shi Bola Tinubu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Tseren Mage: Dakarun soji sun kwato wata bindiga da ake talla, dillalai sun tsere

Tseren Mage: Dakarun soji sun kwato wata bindiga da ake talla, dillalai sun tsere

Tseren Mage: Dakarun soji sun kwato wata bindiga da ake talla, dillalai sun tsere
NAIJ.com
Mailfire view pixel