Hukumar 'yansanda a kasar Scotland ta amince wa ma'aikatanta musulmi sanya hijabi

Hukumar 'yansanda a kasar Scotland ta amince wa ma'aikatanta musulmi sanya hijabi

- Kasar Scotland wadda ke karkashin mulkin Ingila, ta amince da a sanya hijabi yayin aikin dansanda

- Wasu kasashen Turai na kyama da tsoron musulmi, ko addininsu

- Addinin Islama ya tilastawa mata sanya hijabi a waje

Hukumar 'yansanda a kasar Scotland ta amince wa ma'aikatanta musulmi sanya hijabi
Hukumar 'yansanda a kasar Scotland ta amince wa ma'aikatanta musulmi sanya hijabi

Scotland Yard, ita ce hukumar 'yansanda mai kula da dukkan Birtaniya, kasashe hudu da ke karkashin mulkin sarauniyar Ingila. A wannan mako dai, sun amincewa dumbin musulmi mata da suka dauka aiki sanya hijabi muddin suna sha'awar yin hakan.

Wannan wani babban ci gaba ne ga musulmi baqi da ma na cikin gida a kasar ta Ingila, wadanda tuni dama sun sami damar kawo canje-canje sosai a harkokin kasar, kuma har aka samu 'yan Ingila mazauna Landan ma suka zabi Sadiq Khan a matsayin magajin gari.

DUBA WANNAN: Kafin Shekau ya farga, yaransa sun saki kamammu dake hannunsu

Sai dai masu ra'ayin mazan jiya, watau yan Conservative, da ma masu zafin ra'ayin kishin kasa, watau EDL; English Defence League, basu farin ciki da wannan sauyi, inda suke ganin kowanne musulmi a matsayin dan-ta'adda mai mugun nufi, duba da yadda musulman ke mafi yawan kashe-kashen ta'addanci a Yammacin duniya da ma ruguje gabas ta tsakiya baki dayanta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel