Yawan Musulmai na karuwa matuka a fadin Duniya

Yawan Musulmai na karuwa matuka a fadin Duniya

- Kason Musulman da ke Duniya yana karuwa a halin yanzu

- Cikin shekaru 100 addinin ya samu karuwa mabiya a Duniya

- Addinin Kiristanci kuwa na gamuwa da raguwar mabiya ne

Yanzu haka mun samu labari cewa wani bincike na musamman da aka yi ya nuna cewa daga shekarar 1910 zuwa yau, masu shiga Musulmai na kara yawa yayin da ake barin wasu addinan Duniya.

A shekarar 1910 watau sama da shekaru 100 da su ka wuce, yawan Musulman Duniya bai wuce kashi 12.6% ba. A yanzu kuwa da mu ke magana a yau, Musulmai sun mamaye sama da kashi 22.5% na kaf al’ummar Duniya.

KU KARANTA: An yi zaman makokin rashin Mahaifin Janar Buratai

Musulmai na kara yawa yayin da ake barin wasu addinai ne irin su Kiristanci da wasu tsofaffin addinan a kasar China. Daga shekaru 100 da su ka wuce dai zuwa yanzu addinin Kiristanci ya samu raguwar kason mabiya ne.

Yanzu haka dai a wasu sassan Duniya, babu irin sunan da ke tashe irin Muhammaud Nan gaba dai za a cigaba da samun yawan Musulmai a fadin Duniya. Alkaluman World Religion Database ne dai su ka nuna wannan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel