Rikicn dake tsakanin Ali Nuhu da Zango ya zo karshe yayin da aka sasanta su

Rikicn dake tsakanin Ali Nuhu da Zango ya zo karshe yayin da aka sasanta su

- Manyan jaruman Kannywood sun kawo karshen rikicin dake tsakanin Zango da li Nuhu

- A ofishin shugaban hukumar tace fina- finai na jihar kano aka sasanta Ali Nuhu da Zango

Rikicin dake tsakanin manyan jaruman wasan kwaikwaiyon Kannywood Ali Nuhu da Adam zango ya zo karshe yayin da aka sasanta su.

Wannan sasanci ya faru ne bayan kokarin da wasu masu ruwa da tsaki a masana'antar fim Kannywood suka yi.

A gudanar da zaman neman sasanci ne a ofishin shugaban hukumar tace fina- finai na jihar kano Alhaji, Isma'il Na'abba Afakallahu.

Rikicn dake tsakanin Ali Nuhu da Zango ya zo karshe yayin da aka sasanta su
Rikicn dake tsakanin Ali Nuhu da Zango ya zo karshe yayin da aka sasanta su

Cikin jiga-jigan masana'antar Kannywood da suka halarci wannan zaman sasanci sun hada da Falalu Dorayi da Nura husseini, da sakataren kungiyar masu shirya fim Sani Sule Katsina.

KU KARANTA : Dandalin Kannywood: Mansura Isah ta yi wani abun kirki a jihar Kaduna

Falalu Dorayi ya rubuta a shafin sa tare da wallafa hoton su tare bayan kammala zaman neman sasanci.

Suma dai sauran jaruman Kannywood din da suka halarci taron sasanci sun wallafa sakamakon zaman a shafukan sun a sa da zumunta.

Masoyan manyan jaruman biyu sun bayyana farincikin su game da wannan al’amari inda suka yi musu fatan alheri.

Idan aka tuna baya Legit.ng ta taba ba da labarin da, Adam Zango yace sarki Ali Nuhu maigidan sa ne kuma babban wansa ne.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa

Da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel