Sojoji sun tarwatsa makiyaya masu kai hare hare a jihar Benuwe, sun kama guda 2

Sojoji sun tarwatsa makiyaya masu kai hare hare a jihar Benuwe, sun kama guda 2

Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewar jami’anta sun cafke wasu Fulani makiyaya guda biyu a yankin Gbajimba-Iyiodeh dake cikin karamar hukumar Guma na jihar Benuwe, inji rahoton Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito mataimakin daraktan watsa labaru na rundunar Soji ta 707 dake Makurdi, Manjo Olabisi Ayeni yace sun samu nasarar kama makiyayan ne a ranar Talata 6 ga watan Feburairu.

KU KARANTA: An yanke ma matar da ta caka ma Mijinta wuka, hukuncin kisa ta hanyar rataya

Olabisi yace sun kama makiyayan ne yayin da suke gudanar da sintiri a yankin, a lokacin da Sojojin suka hangi makiyayan, suna shirin taruwa a wani daji da nufin kaddamar da hare hare a jihar.

“Mun kama su ne a lokacin da suke taruwa da nufin kaddamar da hari a wata gonar da gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom ke kiwon kifi, da muka nufe su don yi musu tambayoyi, sai suka bude mana wuta, nan take mu ma muka mayar da biki.

“Da suka fahimci mun fi karfinsu, sai suka nemi arcewa, nan fa mu ma muka kara kaimi, inda muka yi nasarar kama guda biyu, yayin da sauran suka ranta ana kare, tuni muka mika wadanda muka kama ga hukumar Yansandan jihar.” iInji Olabisi.

A wani labarin kuma, an cigaba da musayar yawu tsakanin rundunar Yansandan Najeriya da gwamnatin jihar Benuwe, wanda ya yi sanadiyyar shigar majalisar wakilai tsakani, inda tayi kira ga babban sufeta na kana, da ya tsige Kaakakin rundunar daga mukaminsa saboda takalar gwamnan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel