Da Ali Nugu, da Adam A Zango, dukkaninsu Azzalumai ne – Ali Artwork ya ɓara

Da Ali Nugu, da Adam A Zango, dukkaninsu Azzalumai ne – Ali Artwork ya ɓara

Rikita rikita da ya balle tsakanin fitaccen jarumin Kannywood, Ali Nuhu da kuma shahararren dan fina finan Hausa, Adam A Zango, ya janyo cece kuce tsakanin magoya bayansu, kamar yadda Legit.ng ta gano.

Sai dai an samu wani matashin Kannywood, mai tasowa, Ali Artwork yana caccakar dukkaninsu jaruman, inda yace rainin hankali kawai suke yi ma magoya bayansu masu kallon fina finansu.

KU KARANTA: An yanke ma matar da ta caka ma Mijinta wuka, hukuncin kisa ta hanyar rataya

Artwork ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook, inda yace: “Duk abunda kuka ga suna yi (Ali da Adamu) suna sane, kuma da gangan suke kirkirar hakan don su motsa jam’iyya, ka da a ce ai kwana biyu an manta da su. To ku sani, ku Masoyansu ku suka mayar mahaukata.

Da Ali Nugu, da Adam A Zango, dukkaninsu Azzalumai ne – Ali Artwork ya ɓara
Ali Nuhu, Artwork da Zango

“Idan baku manta ba a shekarun baya sun taba shirya irin wannan rikicin, mu ka zo muka yi ta cece kuce a kai. Amma daga karshe mai hakan ta haifar sai suka maida mu ba mu san komai ba. dan haka kusan duk wanda ya sa kansa sai ya yi da na sani.” Inji Artwork.

Jarumin cikin fushi bai tsaya nan ba, har sai da yace: “Ni yanzu babu ruwana da kowa a cikinsu, don a cikinsu babu wanda zai iya kashe min matsalar dubu 200,000. N zauna da kowa a cikinsu, babu wanda bai more ni ba akan harka ta, ta editing. Amma babu wanda na taba yi wa aiki ya dauki dubu dari 100,000 ya ba ni, idan kuma da akwai ya fito ya karyata ni.

“Sai dai kai ta bautar banza. sun fi so kullum ka yi ta ba su girma suna zalintar ka to ku sani an yi walkiya mun ga kowa. Kyar Nake Kallonku. Ba ruwa na da rigimar wani, ni ma ta kaina nake. Idan kana yi da ni, ina yi da kai, idan ba ka yi da ni, ni ma baruwa na da kai.”

Ali ya karkare babatunsa da sakon kai tsaye zuwa ga Ali Nuhu da A Zango, inda yace: “Ku kuma Ali da Adamu duk sanda kuka ga dama ku shirya, ku ta dama ni ko a jikina, ko kuma mutum ya bar industiri din tunda ba da ita aka haife shi ba, don haka mu za mu ciyar da harkar gaba insha Allah, tunda ku sai hassada da munafurci da gwara kan al'umma, ku je ku yi ta yi. Don haka ni na dogara da Allah, shi ne gatana ba wani mutum ba.”

A kwanankin baya ma an samu kace nace tsakanin A Zango da Ali Nuhu, inda A Zango da magoya bayan Ali Nuhu suka dinga musayar yawu da mummunan kalamai, daga bisani ne manya suka shiga tsakani, har aka samu sulhu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel