Dandalin Kannywood: Wani marubuci ya caccaki BMB kan zagi da yayiwa Ali Nuhu na cewa mahaifansa Kirista ne

Dandalin Kannywood: Wani marubuci ya caccaki BMB kan zagi da yayiwa Ali Nuhu na cewa mahaifansa Kirista ne

Wani marubuci mai suna Yakubu M. Kumo ya caccaki BMB kan zagi da yayiwa shahararren jarumin nan na kamfanin shirya fina-finan Hausa Ali Nuhu.

An zargi darakta kuma mai shirya wasa Bello Muhammad Bello da cewa mahaifin Ali Nuhu Kirista ne.

Ga raddin Marubuci Yakubu M Kumo: "Assalamu alaikum ban taba magana akan duk wani al’amari da ya shafi fadan ‘yan fim ba. Sai dai dole na shiga duk wani al’amari da na ci karo da shi, wanda na ke ganin yana bukatar tsokaci a kan addini (duk da dai ni ba malami ba ne).

Na ga wani post da Bello M. Bello ya yi wanda shi a tunaninsa kamar bata sunan Ali Nuhu ya ke son yi, ko kuma martani ne mai zafi ga masoyansa. Sai dai ni a gani na hakan kamar izgilanci ne ga addini, ko kuma shishshigi akan kaddara da nufin Mahaliccinmu.

Dandalin Kannywood: Wani marubuci ya caccaki BMB kan zagi da yayiwa Ali Nuhu na cewa mahaifansa Kirista ne
Dandalin Kannywood: Wani marubuci ya caccaki BMB kan zagi da yayiwa Ali Nuhu na cewa mahaifansa Kirista ne

"Ya kamata Bello ya sani, Ali Nuhu dai Musulmi ne, duk abin da ya haife shi ba zai shafi Musuluncinsa ba, da shi da kai duk daya ne a wajen Allah.

"Don haka ba wani abin fada ba ne don mutum ya kasance Musulmi sannan uba ba Musulmi ba, in har za ka zagi Ali Nuhu saboda wannan sai ka koma ka hada da Annabi Ibrahim, saboda shi mahaifinsa ba ma Kirista ba ne, Kafiri ne mai bautar gumaka (Ka karanta suratul Maryam) Don haka in har Annabi Ibrahim (AS) wanda a tsatsonsa Annabawa kamar su Annabi Musa, Annabi Isma’il, Annabi Isa da Mafificin halitta Annabinmu Muhammad (SAW) suka fito, to waye kuma Ali Nuhu.

KU KARANTA KUMA: Rikicin Benuwe: Sufetan ‘Yan Sanda ba da gaske yake ba inji wata Kungiya

"Saboda irin wannan tunanin ne Allah Ya sake kafa misali a Suratut Tahrim, inda aka nuna matar Annabi Lut ma ba Musulma ba ce, haka kuma dan Annabi Nuhu. Sannan Allah Ya nufi matar Fir'auna da yin imani duk da Kafircewarsa. Kowa da yadda Allah Ya nufa zai zo duniya, kuma babu wanda ya isa ya kaucewa hakan, babu wanda Allah Ya shawarta a lokacin da za a halicce shi, kowa tsintar kansa ya yi a duniyar. Kawai mu yi fatan samun kyakykyawar makoma.

Ba na bangaren kowa, kuma ba na fada da kowa. Bissalam".

Kamar yadda dai kuka sani Ali Nuhu ya kasance jarumi da yayi fice a harkar fim, sannan kuma ya kasance mutun mai tarin masoya.

Ba wai a harkar wasan Hausa kadai Ali yayi fice ba, a'a harma da fim din Kudu.

Har ila yau Ali ya samu lambar yabo da dama kama daga gida Najeriya harma da kasashen ketare.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel