Dandalin Kannywood: Ina matukar son nayi aure - Sadiya Kabala

Dandalin Kannywood: Ina matukar son nayi aure - Sadiya Kabala

A sakamakon yadda ra'ayoyi na rayuwa suke banbanta, wata fitacciyar jarumar fim ta dandalin Kannywood, ta bayyana yadda take matuƙar muradin aure, a yayin da wusu jaruman suke cewa ina ba yanzu ba sai sun shirya zuwa gaba.

Ita dai wannan jarumar ta fina-finan hausa, Sadiya Kabala, ta bayyana irin yadda tale son taga tayi aure a rayuwa, inda har take rokon Mai duka da cewar, Allah ka aurar da mu.

Sadiya Kabala
Sadiya Kabala

Sai dai addu'ar wannan jaruma ba ta taƙaita akan ta kadai ba, inda tayi jimilla wajen rokon Allah, wanda hakan ya nuna ba ita kadai ce jarumar dake buƙatar aure a halin yanzu ba.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Jaruman Kannywood sun karrama shugaban tace fina-finai a jihar Kano

Legit.ng ta fahimci cewa, akwai da yawan jaruman kannywood dake buƙatar aure, sai dai lokaci bai basu ikon samun abokan zama na rayuwar su ba, duba da kasancewar yanayi na rayuwa da mata suke ƙara yin yawa tare da samari ke gudun sa a sakamakon rashin abin hannu.

A baya kadan jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, akwai miliyoyin 'yan mata santala-tala a ƙasar Indiya dake buƙatar aure, sai dai suna kukan cewa har yanzu basu samu mazajen aure ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel