Yanzu Yanzu: shugaba Buhari ya nada Tinubu a matsayin mai sulhu a rikicin APC

Yanzu Yanzu: shugaba Buhari ya nada Tinubu a matsayin mai sulhu a rikicin APC

- Fadar shugaban kasa ta yanke shawarar magance rigingimu a jam’iyya mai mulki wato APC

- Jam’iyyar ta zabi Jigon jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu a matsayin mai sasantawa

- Ana zatton cewa kwarewar Tinubu a fannin siyasa zai inganta mambobin jam’iyyar APC a fadin kasa don hadin kai kafin zaben kasa a 2019

A cikin shirin kokarin inganta hadin kai cikin jam’iyya mai mulki, jam’iyyar APC, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zabi Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da ya jagoranci shawarwari, sasantawa da gina amana a jam’iyyar.

Yanzu Yanzu shugaba Buhari ya nada Tinubu a matsayin mai sulhu a rikicin APC
Yanzu Yanzu shugaba Buhari ya nada Tinubu a matsayin mai sulhu a rikicin APC

Kwarewar Tinubu a fannin siyasa zai inganta mambobin jam’iyyar APC a fadin kasa don hadin kai kafin zaben kasa a 2019.

KU KARANTA KUMA: Bani da laifi, amma zan bari a dama dani – Kakakin IBB

Aikin zai hada da magance rashin yarda tsakanin mambobin jam’iyyar, shugabannin jam’iyyar da masu rike da mukaman gwamnati a wassu jihohin fadin kasar.

Kamar yadda kuka sani a wannan lokaci da ake ciki, jam’iyya mai mulkli ta fada cikin rigingimu a kusan dukkan jihojinta.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa hadimin tsohon shugaban kasa, Ibrahim Babangida, Kasim Afegbua, ya wanke kansa daga laifuffuka, bayan farautar shi da rundunar yan sanda ta sanar da cewan tana yi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel