Manyan jiga-jigan jam'iyyun APC da PDP sun shirya goyon Obasanjo wajen kaddamar da sabuwar jam'iyya

Manyan jiga-jigan jam'iyyun APC da PDP sun shirya goyon Obasanjo wajen kaddamar da sabuwar jam'iyya

A ranar larabar da ta gabata ne, manyan jagorori na jam'iyyun APC da PDP suka ƙulla yarjejeniyar hadin gwiwa da ƙungiyar dake yunƙurin ƙaddamar da sabuwar jam'iyya, wadda tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya ƙuduri kafa wa domin daidaita manyan jam'iyyu biyu na ƙasar nan.

Shugaban wannan ƙungiya, Kanal Olagunsoye Oyinlola, ya bayyana cewa ƙungiyar ta samo tushe ne da sanadin jawaban da shugaba Obasanjo ya gabatar a ranar talatar makon da ya gabata, sai dai ya tabbatar da cewa ƙungiyar ba ta da nufin sabunta wasiyoyi da ƙudirirrikan tsohon shugaban ƙasar.

A yayin haka ne, wata ƙungiyar ƙwararrun masan ta NIM (National Intervention Movement), ta bayyana ƙundirin ta na goyon bayan daidaita manyan jam'iyyun ƙasar nan, inda a ranar da ta gabata ta ce za ta ƙaddamar da hakan a cikin wannan wata.

Olusegun Obasanjo
Olusegun Obasanjo

Daga cikin manyan shahararrun mambobin jam'iyyar APC da suka halarci taron a ranar da ta gabata, akwai Buba Galadaima na kwamitin amintattun jam'iyyar da kuma tsohon gwamna Olagunsoye Oyinlola, shugaban cibiyar samar da shaidar dan kasa da sauran su.

KARANTA KUMA: An ware N4.9bn domin gyaran wutar lantarkin fadar shugaban ƙasa

Daga bangaren jam'iyyar PDP kuma, akwai tsohon shugaban jam;iyyar, Kanal Ahmadu Ali mai ritaya, tsohon gwamna Donald Duke, tsohon an takarar shugaban kasa na jam'iyyar; Dakta Abduljalil Tafawa Balewa da sauransu.

Akwai kuma tsohon shugaban kamfanin dillancin labarai na kasa; Mista Akin Oshuntokun, da ya halarci taron a ranar da ta gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel