Masu garkuwa da mutane sun saki yaron dan majalisa a Zamfara

Masu garkuwa da mutane sun saki yaron dan majalisa a Zamfara

Masu garkuwa da mutane sun saki yaron dan majalisa mai wakiltan mazabar Maradun/Bakura na jihar Zamfara a majalisar tarayya, Alhaji Yahaya Chado bayan mako daya da sace shi.

Kamfanin dillancin Najeriya ta tuna cewa wasu yan bindiga sun yi garkuwa da Muhammad Yahaya da yayansa Junaidu Yahaya a ranar 22 ga watan Janairu a gidansu dake kauyen Gora, karamar hukumar Maradun.

Yan bindigan da suka yi garkuwa da yaran guda biyu sun kuma kashe mutane shida tare da raunata wasu hudu a hanyarsu na fita daga kauyen.

Don haka, masu garkuwan sun saki Mohammed inda sa’a’I biyu bayan haka wata lamba ta kira inda suka bukaci naira miliyan 10 matsayin kudin fansa don su saki Junaidu.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Matsalar zuciya ya kawo cikas a shari’an Fani-Kayode na zambar kudi

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar, DSP Muhammad Shehu, wanda ya tabbatar da sakin a ranar Laraba ya kara da cewa, “bamu da labarin ko an biya wani kudi a matsayin kudin fansa don tabbatar da sakin wanda aka sace”.

An dauki Junaidu wanda masu garkuwan suka ajiye a kauyen zuwa hedkwatan yan sanda dake Gusau domin jin ta bakinsa. “Muna kokarin gano mafakar masu laifin,” cewar shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel