Ziyarar Kwankwaso: Ban yi mamaki ba, dama can na san matsoraci ne – Inji Ganduje

Ziyarar Kwankwaso: Ban yi mamaki ba, dama can na san matsoraci ne – Inji Ganduje

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana su da suka zauna da Kwankwaso tun a baya, kuma suka san halinsa, sun san dama ba zai ziwatar da ziyarar da ya shirya kaiwa jihar Kano ba.

Ganduje ya furta haka ne ta bakin kwamishinan watsa labaru na jihar, Malam Muhammed Garba, wanda yace sun sa abinda Kwankwaso zai iya, kuma sun san abinda ba zai iya ba, kamar yadda ya shaida ma BBC Hausa.

KU KARANTA: Hotunan dan majalisa mai tsawatarwa a majalisar wakilai yayin da yake jagorantar matasa ɗauke da muggan makamai

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kwamishinan na fadin “Tun lokacin da kwankwaso ya sanar da ziyarar da zai kai jihar Kano, ya san ba zai yiwu awaitar da ita ba, don kuwa shi mutum ne mai tsoro matsoraci ne.”

Sai dai Kwamishina Garba ya musanta ikirarin da Kwankwaso ya yi na cewa wai shuwagabannin ne suka shiga tsakaninsu, har ta sanya shi janye tafiyar, musamman fadar shugaban kasa. Kwamishinan yace karya ne, babu wanda ya gayyace su fadar shugaban kasa kan wannan batu.

“Babu wanda ya shiga tsakaninmu da Kwankwaso, ba fadar shugaban kasa ba, kuma ba wasu shuwagabanni ba, don haka ba gaskiya bane da yace fadar shugaban kasa ne ta bashi shawarar ya janye, ai da ace ya je fadar shugaban kasa kan batun nan, da an watsa shi a yanar gizo.” Inji Garba.

Daga karshe Kwamishinan ya bayyana jami’an tsaron da rundunar Yansanda ta jibge a matsayin wajibi don gudun ko ta kwana, musamman daga bangaren Sanata Kwankwaso, ta yadda zasu yi maganin masu tayar da hankali.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel