Wasikar Obasanjo: Talakawa ne zasu zabe mu ba attajirai ba – Inji Gwamnan jihar Kaduna

Wasikar Obasanjo: Talakawa ne zasu zabe mu ba attajirai ba – Inji Gwamnan jihar Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmed El-Rufai ya mayar da martani game da wasikar da tsohon Maigidansa, kuma tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya rubuta ma Buhari.

A cikin wasikar da ta tayar da kura, Cif Obasanjo ya ja hankalin shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan cewa kada ya kuskura ya sake tsayawa takara a karo na biyu a shekarar 2019, a cewar Obasanjo, Buhari ya gaza.

KU KARANTA: Abin da ya sa nake buga Turanci na babu ruwa na – Hon. Gudaji Kazaure

Sai dai gwamnan jihar Kaduna, El-Rufai ya bayyana cewa wasikar Obasanjo ba ta da wani tasiri, kuma babu wani tasirin da za ta yi a zaben shekarar 2019, inda yace Talakawa ne zasu yi zabe, ba attajira da sauran manyan mutane ba.

Wasikar Obasanjo: Talakawa ne zasu zabe mu ba attajirai ba – Inji Gwamnan jihar Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna

NAIJ.com ta ruwaito gwamnan yana fadin: “Ban samu sukunin karanta wasikar Obasanjo ba, saboda tana da tsawo, kuma ni kai na da hidima sosai a gabana. Amma fa bani da wani shakku game da 2019, zamu lashe zaben shugaban kasa a 2019.

“Na tabbata zamu ci jihohin mu 24, har ma da kari, akwai rukunin mutane guda biyu a Najeriya, Attajirai da Talakawa, da ikon Allah talakawa zasu samu nasara a 2019.”

Tun bayan fitar wasikar ne dai ake ta dakon martanin da gwamna El-Rufai zai mayar, duba da alakar dake tsakaninsa da tsohon shugaban kasa Obasanjo. Ita ma fadar shugaban kasa a nata martanin tace watakila Obasanjon bai samu lokacin bibiyan abubuwan dake faruwa a Najeriya bane, shi yasa bai san Nasarori da cigaban da gwamnatin Buhari ta samu ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar NAIJ.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dalilin da yasa dole Saraki zai yi murabus daga kujerarsa - Gbajabiamila

Dalilin da yasa dole Saraki zai yi murabus daga kujerarsa - Gbajabiamila

Dalilin da yasa dole Saraki zai yi murabus daga kujerarsa - Gbajabiamila
NAIJ.com
Mailfire view pixel